FILATO: Karfin addu’a ta sa barayin da su ka saci kayan tallafi suka rika maidawa da kan su

0

Wasu da su ka saci kayan tallafin korona a lokacin tarzomar #EndSARS a Filato, sun rika maida kayan da su ka sata da kan su.

A jihar Filato dai wasu daga cikin hukumomin da aka ragargaza aka sace kayayyakin, sun hada da Runbun Ajiyar Kayan Abinci na SEMA,
PRUWASSA, PADP, ASTC, SUBEB, Makarantar Sakandare ta Fasaha a Bukuru, sai kuma wasu wurare da dama, ciki har da gidan tsohon kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara.

Ranar Litinin sai da PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito cewa mazauna yankin Riyom sun gamu da cuta sanadiyyar cin kayan tallafin da ya rube.

An saci kayayyakin da aka adana bayan an sa masu sinadarin kashe kwari da beraye mai guba don kada su rube.

Akalla mutum 20 aka gaggauta wa yi magani bayan sun kamu da cutar abinci mai guba, jim kadan bayan sun Kwankwadi kunun da aka yi gero.

Mutanen duk ‘yan cikin kauyen Joi ne da ke karkashin Karamar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.

Cikin wadanda su ka kamu da ciwon har da basaraken kauyen, Stephen Jogu. An ce a hannun wani mutumi aka sayo geron kwanaki kadan kafin kamuwa sa cutar.

Jugu wanda kuna shi ne Shugaban Mabiya COCIN, ya shaida cewa shi ma ya na cikin wadanda aka yi wa maganin cutar, tare da mutane 20.

“Na farka da tsakar dare na rika zawayi, washegari na gano ashe mu na sa yawa. Mun fi mutum 20. Amma duk an sallame mu.

Wani mai suna Tim Danchal ya ce wasu da su ka sha kunun sun rika tsula zawayi, har sai da su ka suma.

Ya kara da cewa wasu had aman jini su ka rika yi. Amma dai duk an suba su.

Wani jami’in Lura da Cuta Mai Yaduwa, Livinus Miskoom, ya danganta cutar daga cin abinci mai guba wanda aka yi wasaso a Filato. Ya yi gargadin a guji cin irin wannan abinci.

An sai daka wasoson kayan abinci a wurare mallakar gwamnati da sauran jama’a. Ciki kuwa har da gidan tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara.

Sanarwar baya-bayan nan da kakakin gwamna Simon Lalong, Makud Simon Macham ya fitar, ya ce wasu barayin da dama sun mayar da kayan sa su ka sata da kan su. Kuma su ka roki a yafe masu abin da su ka yi bisa kuskure da kuma rudin zuciya.

Macham ya ce wani babban limanin darikar COCIN, mai suna Ezekel Dachomo ne ya jagoranci tubabbun barayin kayan satar zuwa Fadar Gwamnan Jihar Filato, domin Gwamnatin Filato din ta yafe masu.

Dachomo ya ce barayin sun zo wurin gangamin tuba a harabar Sakandare ta Zang da ke Bukuru, cikin Karamar Hukumar Jos ta Kudu, su ka tuba.

Ya ce sama da mutum 2000 su ka kawo kan su, bayan sun saurari wa’azin da ya yi a lokacin, inda ya jaddada masu fushin ubangiji kan wadanda ke lalata dukiyoyin jama’a.

PREMIUM TIMES ta gano cewa akasarin kayan da aka maida duk kayan abinci ne.

Share.

game da Author