KORONA: An samu karin mutum 152 da suka kamu a Najeriya ranar Talata

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 152 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –61, Oyo-39, FCT-13, Yobe-10, Bauchi-6, Kaduna-5, Kano-4, Kwara-4, Filato-4, Edo-2, Ogun-2, Rivers-2.

Yanzu mutum 65,457 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 61,337 sun warke, 1,163 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,957 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,562, FCT –6,385, Oyo – 3,693, Edo –2,690, Delta –1,823, Rivers 2,916, Kano –1,768, Ogun –2,103, Kaduna –2,778, Katsina -965, Ondo –1,722, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 750, Ebonyi –1,055, Filato -3,724, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –648, Jigawa – 325, Kwara –1,088, Bayelsa – 426, Nasarawa – 485, Osun –942, Sokoto – 165, Niger – 283, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 92, Ekiti – 346.

Taraba- 153, Kogi – 5, da Cross Rivers – 89.

A ranar 11 ga Nuwanba ne kamfanin Pfizer dake kasar Amurka da Kamfanin BioNTech dake kasar Jamus suka Sanar cewa sun hada maganin rigakafin kamuwa da kwayoyin cutar korona dake da aka tabbatar da ingancin sa da akalla kashi 90 bisa 100.

Wadannan Kamfanonin sun hada wannan magani ƙasa da lokacin da ake zaton za a kammala hada shi kuma har sun yi gwajin ingancin sa a jikin mutane sama da 44,000.
Kamfanonin na sa ran cewa gwajin ingancin maganin da ake yi ba zai dauki tsawon lokaci ba domin samun izinin fara amfani da maganin.

Hada maganin cutar korona

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ce kungiyar dake kula da ingancin magungunan da masana kimiya a fadin duniya ke kokarin hadawa.

Bisa ga ka’ida hada maganin zai dauki tsawon shekara daya da wata shida ne.

Kungiyar na sa ran samun biliyoyin ruwan maganin nan da shekara 2021 domin raba wa kasashen duniya.

Zuwa yanzu akwai Kamfanonin 150 dake himman suma su hada maganin korona a duniya, sai dai kuma da kyar za a samu guda daya dake da ingancin kawar da cutar a wanna shekara.

Burin WHO shine samar da maganin dake da ingancin kashe kwayoyin cutar korona ba tare da ya cutar da kiwon lafiyar mutane ba.

Share.

game da Author