Babu jirgin da Boko Haram suka harbo a Maiduguri – Rundunar Sojin Sama

0

Rundunar sojin saman Najeriya ta karyata labaran da aka rika yadawa wai Boko Haram sun harbo wani jirgin yaki a garin Banki, dake jihar Barno.

A wata takarda da rundunar ta fitar ranar Talata, Ta ce jirgin majalisar Dinkin Duniya ne ya yi shawagi a sararun saman garin Banki a lokacin da ya je yin wani aiki na musamman.

A cewar takardar, jirgin ya koma garin Maiduguri lafiya lau ba tare da ya samu wani tangarda ba a lokacin aikin.

Haka kuma kungiyar bada agaji na ajalisar Dinkin Duniya, UN ta tabbatar cewa lallai jirgin su ya tafi garin Banki, amma kuma ya dawa lafiya lau garin Maiduguri.

Sai dai kuma an samu tabbacin rahotanni daga bakin kungiyar UN din cewa jirgin yayi saukar gaggawa a Banki bayan ya samu matsala a sama. Bayan haka aka duba jirgin sannan ya koma Maiduguri.

Share.

game da Author