Bayan samun rahotan sace shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa da mahara suka yi da daren ranar Asabar a lafiya, an tsinci gawarsa ranar Lahadi.
Mahara sun afkawa gidan shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa Philip Shekwo, ranar Asabar da Dare a gidan sa dake Lafiya suka yi awon gaba da shi.
Wani jigo a jam’iyyar APC na jihar, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES aukuwar hakan da kuma tsintar gwarasa da ka yi.