A karamar hukumar Guri dake jihar Jigawa gwamnati ta yi wa yara 46,634 allurar rigakafin cutar Shan Inna.
Jami’in yada labarai na hukumar Sunusi Doro ya fadi haka wa manema labarai ranar Juma’a a garin Dutse.
Doro ya ce an yi amfani da kwalaben ruwan maganin rigakafi 49,260 wajen yi wa yara rigakafin cutar da wasu cututtukan a karamar hukumar.
Sannan kuma ya yabawa sarakuna kan goyon baya da suke ba malaman asibiti a lokacin yin rigakafin.