Shugaban sashen tsaro na jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Ashiru Zango, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa mahara sun saki daliban jami’ar su 9 da suka sace a titin Kaduna-Abuja.
Sai dai kuma ya ce bai samu cikakken yadda aka yi da maharan ba tukunna, amma kuma Jaridar Express ta ruwaito cewa sai da aka biya naira miliyan 1 kan kowani dalibi kafin a sake su su 9.
Yadda aka sace daliban jami’ar ABU a titin Kaduna-Abuja
Daya daga cikin daliban da aka sace wanda dukkan su na karatu ne a sashen koyan harshen faransanci a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya shaida cewa shi da direban motan da wani dalibi suka tsira a hannun maharan
Dalibin mai suna Dickson Okoh ya ce da shi da direban da abokin sa da suka tsira sun samu rauni a jikin su.
Okon ya kara da cewa maharan sun bukaci a biya wa kowani dalibi naira miliyan 30 kudin fansa, su tara dake tsare a hannun su.
Su dai wadannan dalibai sun baro Zariya ne akan hanyar su ta zuwa Legas su 12 a bus kirar Hiace.
Direban motan mai suna Nuruddeen Mohammed ya shaida wa Daily Trust cewa ko da suka isa garin Akilibu Gidan Busa dake titin Kaduna-Abuja sai suka fada wa maharan.
Mohammed ya ce sun rika harbi da bindiga ta ko ina a duka hanyoyin biyu wato na tafiya da na dawowa.
Ya ce suma arcewa suka yi ciki daji da gudun tsiya har Allah ya basu sa’a suka tsira.
Duk da cewa kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan da Kakakin gwamnatin Kaduna Muyiwa Adekeye, basu ce komai a kai ba, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya ce ƴan sanda na farautar wadannan mahara a yanzu haka.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda masu garkuwa suka yi garkuwa da ƴan sanda 12 a hanyar su ta zuwa garin Gusau daga Jihar Barno.
Haka kuma an ruwaito yadda mahara suka tsare hanyar Kaduna- Abuja har sau hudu a yini daya.