A zaben da za a kafsa yau Asabar domin fitar da Gwamna a Jihar Ondo, akwai muhimman batutuwa 20 da masu karatu ya kamata su sani:
1. Jam’iyyu 17 ne za su yi takarar zaben gwamna a Jihar Ondo, amma guda uku ne masu karfin iya lashe zabe.
Su ne jam’iyyar APC wadda Gwamna Rotimi Akeredolu ya sake tsayawa, bayan ya yi nasara a 2016.
Sai Eyitayo Jegede na PDP, wanda shi ne Rotimi ya kayar a zaben 2016.
Sai Agbola Ajayi, wanda shi ne Mataimakin Rotimi a zaben 2016. Yanzu kuma ya fice daga APC, ya taya a karkashin jam’iyyar ZLP, bayan da ya koma PDP ta ki tsayar da shi takara.
2. Dukkan manyan ‘yan takarar uku gogaggun lauyoyi ne. Rotimi da Jegede sun kai matsayin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN).
3. Manyan ‘yan takarar uku kowa daga shiyyar Sanata daban-daban su ka fito. Rotimi daga Shiyyar Ondo ta Arewa, Jegede daga Ondo ta Tsakiya, Ajayi daga Ondo ta Kudu.
4. Jegede dan takarar PDP ya taba rike mukamin Kwamishinan Shari’a na Jihar Ondo.
5. Shiyyoyin Sanatocin Ondo uku, kowace Kananan Hukumomi 6 ne a karkashin ta.
6. Akwai Kananan Hukumomi 18 a Jihar Ondo.
7. Mutum 1,822,346 su ka yi rajista da INEC, amma mutum 1,478,460 ne su ka karbi katin rajista.
8. Akwai Mambobin Majalisar Tarayya su 9 masu wakiltar Jihar Ondo.
9. An kirkiro Jihar Ondo a zamanin mulkin soja na Marigayi Murtala, a ranar 3 Ga Fabrairu, 1976.
10. Lissafin Kidayar Jama’a na 2006 ya nuna akwai jama’a 3,460,877 a Jihar Ondo.
11. Jihar Ondo na da mazabu 203, sai kuma rumfunan zabe guda 3,009.
12. Ondo ta yi iyaka da Jihohin Ekiti, Kogi, Edo, Delta, Ogun da Osun.
13. Ogun ta yi mashahurai da dama, kakar Gani Fewehenmi, T.B Joshua, Gani Adams, Oyelere Sowore da sauran su.
14. Kabilar Yarabawa ne al’ummar Ondo. Su din ma sun kasu zuwa Yarabawan Akuka, Akure, Ikale, Ilafe, Ondo, Owo. Amma akwai tsirarun kabilar Ijaw ‘yan asalin jihar.
15. Ondo na da arzikin man fetur.
16. Ondo Jihar ‘Yan Boko: Akwai jami’o’i har takwas a jihar Omdo. Sun kunshi Elizade University, FUT Akure, Adekunle Ajasin University, Jami’ar Kimiyya Da Fasaha ta Jihar Ondo, Achievers University, Wesley University of Science and Technology, University of Madical Science da kuma National Open University of Nigeria (NOUN), Akure.
17. Akure ne babban birnin Jihar Ondo.
18. Adekunle Ajasin ne gwamnan farar hula na farko a Jihar Ondo. Ya yi mulki daga 1979 zuwa 1983, lokacin da sojoji su ka yi juyin mulki.
19. Sunan Gidan Gwamnatin Ondo Alagbaka Government House.
20. Sowore, mawallafin Sahara Reporters, wanda a yanzu ke jan zugar zanga-zangar neman a rushe ‘yan sandan SARS, dan asalin jihar Ondo ne.
Discussion about this post