Kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta yi a zaben gwamnan jihar Edo da ma sauran zabukan da su ka gabata, a wannan zaben na jihar Ondo ma ta tura wakilai masu dimbin yawa a lunguna, kauyuka, garuruwa na jihar.
Tun a ranar Juma’a su ka isa ofisoshin jami’an zabe na Kananan Hukumomin jihar 18, su na kallon yadda jami’an INEC tare da jami’an tsaro ke aikin rarraba kayan zabe zuwa mazabu daban-daban.
Rahotannin da su ka fara aikowa tun da safiyar Asabar, sun bayyana yadda aka fara kai kayan zabe a rumfunan zabe tun da safe.
Yawancin rumfunan da su ka gane wa idon su, an kai kayan zabe kuma akwai jami’an tsaro a wurin.
Yayin da tuni aka fara jefa kuri’a a wasu rumfuna, wakilan mu sun lura cewa a kan bar dattawa maza da mata masu shekaru da yawa su fara jefa kuri’a rukunna.
Sai dai kuma wakilan mu sun nuna cewa yawancin rumfunan zabe jama’a sun ki bin ka’idar barin tazara tsakanin juna, wadda Hukumar Dakile Cutar Korona (NCDC) ta gindaya.
Duk da haka su kuma jami’an INEC sun rika cewa tilas sai mutum ya daura takunkumin baki da hanci sannan zai matsa ya jefa kuri’a.
Zaben Jihar Ondo wanda jam’iyyu 17 su ka shiga takara, APC, PDP da ZLP ne kadai masu karfin iya cin zabe.
Gwamna Rotimi Akeredolu na APC zai fafata da Eyitayo Jegede na PDP, wanda ya kayar a zaben 2016.
Dan takara mai karfi na uku shi ne Agbola, Mataimakin Gwamna, wanda ya fice daga APC ya koma ZLP.
Kowanen su ya na da karfi a Shiyyar Mazabar Sanatan sa.