Yadda Boko Haram su ka guntule kan manoma 13 a Barno

0

Cikin makonni biyu da su ka gabata dai Boko Haram sun rika tattaki har cikin gonaki su na kashe manoma a yayin da su ke girbin amfanin gonar su.

Akalla manoma 13 Boko Haram su ka fille wa kai lokacin da su ke girbin amfanin gona, a cikin kauyukan da ke gefen Maiduguri, babban birnin Jihar Barno. Lamarin kamar yadda wadanda su ka ga gawarwakin da su kuma jami’ai su ka tabbatar, ya auku ne cikin makonni biyu da su ka gabata.

PREMIUM TIMES ta samu cikakken labari daga majiyar da ta tabbatar, kan yadda rayuwar manoma ke ci gaba da shiga hadari a kowace rana, saboda hare-haren kisan-gilla da ‘yan ta’adda ke kai masu.

A farkon wannan shekarar ce Gwamnatin Barno ta kaddamar da Shirin Kare Rayukan Manoma (Agro Rangers Programme), wanda ya kunshi jami’an tsaron ‘yan sanda da na ‘yan bijilante, inda su ke aikin tsaron manoma a ginakin da ke kusa da kuma kewayen Maiduguri.

Sai dai kuma mummunan hare-haren da ake kai wa manoma a kai a kai, na nuna an ci karfin wadannan rundunar kare manoman karkara kenan.

“An kashe manoma shida a ranar Litinin, 19 Ga Oktoba, a cikin gonakin da ke hanyar Auno daga Maiduguri. Garin Auno na kan titin zuwa Kano daga Maiduguri.”

Haka dai wani dakaren Maida Farmakin Gaggawa (Rapid Response Squard), mai suna Bunu Mustapha ya shaida wa PREMIUM TIMES.

“Biyar daga cikin manoman guntule masu kai aka yi, dayan kuma mai shekaru 45, ta baya aka harbe shi da bindiga a lokacin da ya ke kokarin tserewa.”

Majiyar PREMIUM TIMES ta ci gaba da cewa mutum hudun da aka fille wa kai duk ‘yan gida days ne. Sauran biyu kuma ‘yan aiki ne, wato leburorin da aka kira domin taya su aikin girbin amfanin gona.

“Ka san yanzu an shiga kakar girbe amfanin gona, yawancin manoma kuma duk sun tattara amfanin noma su na shirin kwashewa su kai gida. Sai dai kuma Boko Haram sun hada su cin abin da su ka noma, su ka girba.”

Har yanzu tsakanin ‘yan sanda ko sojoji, babu wanda ya yi magana a kan wannan mummunan kisa da aka yi wa manoma.

Kusan mako daya bayan fille kan wadancan manoma, Boko Haram sun sake kashe wasu manoman, a ranar Asabar, a kewayen kauyen Moromti, wajen da su ka yi wancan ta’addanci na farko.

Majiyar da ta san labarin kisan ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa wasu manoma tara sun fada tarkon Boko Haram a kan hanyar su ta zuwa gonakin su.

“An samu gawarwakin shida an fille masu kai, sauran uku kuwa har yau ba a san yadda aka yi da su ba. Idan sun tsira, har yau babu labari. Idan an kashe su, to an nemi gawarwakin an rasa. Idan kuma an yi gaba da su, duk dai babu labari.”

Haka wani mutumin da ke zaune a kauyen Auno mai suna Muhammad Bashir ya shaida wa PREMIUM TIMES.

“Wato gawarwakin manoman nan shida ba su da kyawon gani. Sai da mu ka kira jami’an C-JTF sannan aka samu su ka danna cikin daji, su ka kwaso gawarwakin.”

Karamin Ministan Harkokin Noma, Baba Shrhuri, ya tabbatar da kisan manoman, a lokacin da ya ke taro da masu ruwa da tsaki a harkokin noma, ranar Asabar a Maiduguri.

“Yau da rana din an a lokacin da na ke kan hanyar zuwa wannan taro, na samu labarin kisan-gillar da Boko Haram su ka yi wa manoma takwas aka ce ko tara, a lokacin da su ke aikin girbin amfanin gona.” Haka Minista Shehuri ya fada a wurin taro, wanda shi ma dan asalin Jihar Barno ne.

“Wannan abu ya yi muni, kuma ya nuna irin gaskiyar lamarin halin da mutanen mu ke ciki a wannan jiha.” Inji shi.

Mugun Ji Da Mugun Gani: Ganawar PREMIUM TIMES Da Dangin Mamatan:

Sadiq Abubakar dan’uwa ga manoma hudu daga cikin shidan farko da aka fille wa kai. Lokacin da wakilin PREMIUM TIMES ya yi tattaki har gidan a kauyen Bulabulingaranam, ya kara yi masa cikkakken bayani.

Kauyen ba shi da nisa daga Maiduguri.

A baya, kauyen Bulabulingaranam mabuyar ‘yan Boko Haram ce, kafin a fatattake su cikin 2013.

Sadiq ya ce dangin da aka kashe din duk mazauna sansanin gudun hijira ne (IDPs), a Bulabulingaranam, bayan garin Maiduguri.

“Sun tafi girbin amfanin gonar su a ranar Litinin. Ashe tafiyar ba ta dawowa gida ba ce.” Inji shi, a cikin takaici.

Ya ce sun shafe kwanaki su na girbin amfanin gonar su a kusa da Moromti.

“A ranar da aka kai masu hari, ashe Boko Haram sun yi masu kwanton-bauna a cikin gonar, su na jiran su karasa, su dirar masu.”

“To cikin masu aikin gonar akwai mata. Lokacin da Boko Haram su ka kewaye su, sai su ka ware matan da ban a gefe daya. Su ka ce masu idan ku na so wadannan mazan su dawo da ran su, to kada wacce ta matsa daga nan wurin har sai sun dawo daga inda za mu tafi da su.

“A haka matan nan su ka zauna a gona, zaman jiran dawowar mazan da Boko Haram su ka yi gaba da su, su shida. Sun jira har dare ya yi, amma babu alamar su.

“Washegari ranar Talata, sai matan kauyen su ka shigo gari, su ka samu jami’an tsaron da ke kan titi, su ka shaida masu abin da ya faru. Daga nan jami’an su ka shiga daji bin-sawu, har su ka cimma wurin da su ka ga gawarwakin su.

“Dukkan wadanda aka kashe din an fille masu kai, in banda babban cikin su, wanda ya fi sauran yawan shekaru. Sai da aka dauki tsawon lokaci a cikin daji, ana neman kiren kan kowanen su, kafin a samu a tsinto su.

“Da kyar aka samu aka sa su kabari, saboda gawarwakin duk sun fara rubewa, saboda tsananin zafin da mu ke fama da shi.”

Allah kadai ya san yawan mutanen da Boko Haram su ka kashe tsakanin Auno da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Kano, da Moromti da Bulabulingaranam.

Share.

game da Author