Gwamna Nyesom Wike na Ribas, ya tabbatar da kafa dokar da ta haramta kungiyar ‘yan kabilar Igbo zalla, masu hankoron ballewa daga Najeriya, IPOB a jihar.
Kakakin Yada Labarai na Gwamna Wike, Kelvin Ebiri ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya aika wa manema labarai a ranar Alhamis.
Ebiri ya ce kamar yadda Gwamna Wike ya shaida a jawabin da ya yi wa al’ummar Jihar Ribas kai-tsaye ta radiyo da talbijin, ya nanata cewa Jihar Ribas jiha ce ta dukkan kabilun kasar nan, ba ta wata kabila daya tal ba.
Ya ce Gwamnatin Ribas ta na jinjina wa kikari da gudummawar da wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ke bayarwa wajen bunkasa da cigaban siyasa, rayuwa da tattalin arzikin jihar.
Sai dai kuma sanarwar ta ci gaba da cewa Jihar Ribas ba za ta amince wani gungu ko wani mutum ko kungiyar ‘yan cikin gida ko na waje su hargitsa zaman lafiya da rayuka da dukiyoyin jama’a, bisa fakewa da sunan wata kungiyar ko rukuni ko gungun wasu tsiraru ba.”
“Gwamnatin Jihar Ribas ta haramta duk wani motsi ko taro da ma kungiyar nan haramtacciya ta IPOB masu tada zaune tsaye a Jihar Ribas.
“Don haka daga yau kowa ya sani kungiyar masu kumajin kafa Biafra ta IPOB ce kawai mu ka haramta, amma ba mu da wata nifada ko mugun nufi kan wata kabila. Kuma za mu ci gaba da bude hannaye bib-biyu mu karbi kowace kabila tare da tafiya tare a Jihar Ribas.
“Amma ba za mu taba amincewa da numfasawar haramtacciyar kungiyar IPOB ta kabilar IPOB zalla a Ribas ba.
Wike ya yi sanarwar dage dokar-ta-baci da ya kafa a wasu yankunan Fatakwal.
Ya kuma hana masu KEKE NAPEP zirga-zirgar jigilar fasinja a manyan titinan Fatakwal.
Discussion about this post