Mahara sun kashe mutum 21 a jihohin Katsina da Zamfara

0

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Katsina Gambo Isah a ranar Alhamis ya bayyana cewa mahara sun kai wa kauyen Diskuru dake karamar hukumar Dandume harin ramakon gayya Inda akalla mazaunan kauyen 12, ‘yan kungiyan ‘yan banga hudu da dan sanda daya suka mutu.

Isah ya ce maharan sun dawo wannan kauye domin ramuwar gayya ne, bayan sun yi arangama da ‘yan bangan garin a makon da ya wuce.

A jihar Zamfara mahara sun kashe mutum hudu sannan uku sun ji rauni a kauyen Gidan-Goga dake karamar hukumar Maradun.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammed Shehu ya ce gaggauta zuwa kauyen da jami’an tsaro suka yi ya taimaka wajen rage yawan rayukan da aka rasa a kauyen.

Mutum uku din da suka ji rauni na samun kuka a asibitin FMC Gusau.

Shehu ya ce an aika da jami’an tsaro zuwa wannan kauye domin samar wa mutanen kauyen tsaro.

Share.

game da Author