KORONA: Jami’an Lafiya sun yi kukan hana su kudaden alawus bayan rufe cibiyoyin killace majiyyata

0

Watanni biyu bayan kulle cibiyoyin killace masu fama da cutar korona a Abuja, babban birnin tarayya, jami’an kiwon lafiya da su ka yi aiki a wuraren sun koka cewa watanni uku kenan an ki biyan su kudaden alawus-alawus din su.

PREMIUM TIMES ta bada rahoton yadda aka kulle cibiyoyin killace masu cutar korona da ke Karu da Asibitin Asokoro, saboda babu wadanda za a rika killacewa a ciki.

Wakilin mu da ya je cibiyar killace masu cutar korona a Karu, ya same ta a kulle. Haka ita ma cibiyar da ke Asokoro, a kulle ya same ta.

Jami’an gwamnati sun ce sun yanke ahawarar kulle cibiyoyin biyu na Karu da Asokoro ne, amma sun bar ta Edu da ta Dandalin THISDAY.

Sakataren Kula da Harkokin Lafiya na FCT, Mohammed Kawu, ya ce dama wuraren ba su dace a rika killace masu cutar korona a ciki ba, domin ba a gina su a kan haka ba. Shi ya sa aka kulle su.

“Za mu maida su kamar yadda su ke, wato asibitoci. Kuma mun cimma haka tun a ranar 24 Ga Augusta. Saboda mun ga cewa yawan wadanda ake samu dauke da cutukan duk raguwa su ke ta yi.

Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES a tattaunawar da aka yi da shi.

An Bar Jami’an Lafiya Cikin Halin Kaka-ni-ka-yi:

Wani jami’in kula da tsaftace cibiyar killace masu korona a Karu, mai suna Aliyu Saidu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa har yau ba a shaida masu dalilin kin biyan su alawus din watan Yuni, Yuli da na Augusta ba. Sannan kuma ba a sanar da su cewa za a rufe cibiyar ba.

Ma’aikatan wurin masu yawa sun tabbatar da cewa ba a biya su kudin watanni uku ba. Amma sun ce ba za su iya yin korafi kamar yadda Aliyu Saidu ya yi ba, saboda su na aiki ne a karkashin hukumar FCT. Idan su ka yi magana da dan jarida, za a iya yi masu bi-ta-da-kulli.

Sai dai Mohammed Kawu ya ce wa wakilin mu akwai jami’ai masu aiki a cibiyar warkar da masu korona, wadanda ya ce duk an biya su har da alawus din watan Agusta.

“Saboda haka idan wani ya ce ba a biya shi ba, to ba gaskiya ba ne.”

“Hukumar FCT na biyan kowane likita naira 50 duk rana. Mai kula da bada magani N30,000 a kullum. Su kuma masu shara da direbobi naira 20,000 kowanen su a kullum.”

Wasu da aka yi hira sa su, sun rantse sun ce maganar da jami’in lafiya Mohammed Kawu ya shaida wa PREMIUM TIMES, ba gaskiya ba ce.

“Jihar Nasarawa na baro inda iyali na su ke don na yi wannan aikin. Kuma ni da sauran mu da yawa tun alawus din Mayu ba a sake bilyan mu ko sisi ba.” Inji wani mai korafin.

Share.

game da Author