KASAFIN 2021: Hasashe Da Kintacen Kudaden Da Za Mu Samu Da Wadanda Za Mu Kashe -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kintacen cewa Najeriya za ta tara kudaden haraji har naira tiriliyan 8.433 a cikin 2021.

Ya ce daga cikin wadannan kudaden za a kashe naira tiriliyan tiriliyan 7.886 wajen Kasafin 2021. Amma daga cikin akwai kudaden agaji da tallafin da manyan cibiyoyi na duniya kan bayar, har naira bilyan 354.85.

Sannan kuma akwai kudaden shiga da za a karba a hukumomin gwamnatin tarayya har 60.

Buhari ya ce ana kintacen tara kudin shiga daga ribar fetur har naira tiriliyan 2.01. Sauran kudaden shigar da ba na fetur ba kuwa, ana sa ran za a tara naira tiriliyan 1.49.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya cewa Ministar Harkokin Kudade Da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ce za ta yi wa Majalisa bayani dalla-dalla na abin da kowane bangaren kasafin ya kunsa.

Buhari ya fadi haka ne da ya ke gabatar da kasafin kudi na 2021 a zauren majalisar Tarayya ranar Alhamis.

” Mun gabatar da Kasafin 2021 a daidai lokacin da duniya ke fama da gaganiyar annobar cutar korona, wadda sanadiyyar hakan ta haifar da karyewar farashin danyen man fetur, abin da hakan kuma ya kawo cikas ga tattalin arziki.

“Tattalin arzikin Najeriya ya samu tawaya domin karin tattalin arzikin cikin gida (GDP) ya ragu da kashi 6.1 a watanni Afrilu, Mayu, Yuni da Yuli na shekarar 2020. Amma duk da haka, karfin tattalin arzikin Najeriya ya fi na sauran manyan kasashen duniya da kasashe masu tasowa karfin jure dadin kibiyar matsalar da annobar korona ta haifar a duniya.

Daga nan sai ya kara da cewa Gwamnati ta kirkiro aikin-karfi ga matasa 774,000 a fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan domin rage kuncin rayuwa.

” Mun kuma kirkiro Shirin Tallafa wa matasa da naira bilyan 75. Tuni ma har an saka naira bilyan 25 daga cikin kudaden Kasafin 2021 domin a fara yin somin-tabi sa su.

Share.

game da Author