Nasarorin da muka samu a Kasafin 2020 – Buhari

0

Mun ci gagarimar nasara a Kasafin 2020.

Kuma farin ciki na shi ne kun sha jin bayanan ayyukan da aka yi, wasu kuma duk an gan su.

Ayyukan Noma

Mun samu gagarimar nasara a Shirin Bada Lamuni na Anchor Borrowers Programme da Shirin Tallafin Takin Zamani na Ofishin Shugaban Kasa a karkashin CBN. Akwai kuma shirin NSIA.

Sannan mun gina kananan titina har 337 a yankunan karkara masu albakar hada-hadar noma.

Ci Gaba A Sufurin Jiragen Kasa

Mun kammala aikin titin Lagos zuwa Ibadan. Kwanan nan zai fara aiki. Na Abuja zuwa Kaduna kuwa na nan na ci gaba da zirga-zirga. An kammala titin Itakpe zuwa Ajaokuta, bayan shekaru 30 da bayar da aikin. Mun bude shi tun a cikin Satumba, 2020.

Ana tsare-tsaren yadda za a fara aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano da na Fatakwal zuwa Maiduguri. Da na Kalaba zuwa Lagos.

Aikin Zankaleliyar Gadar Kogin Neja: Wannan gagarimin aiki har an kammala kashi 46% bisa 100%. Kuma mu na sa ran kammalawa da bude gadar a nan da 2023.

Mun kuma bada aikin da ake ci gaba da gina manyan titinan gwamnatin tarayya da gina gadoji.

A karkashin shirin RITCS kuma mu na kan aikin gyaran titina masu jimillar tsawon kilomita 780 a fadin kasar nan. Aikin ya tafiya kafada-kadafa da aikin gyaran gadojin da ke kan hanyoyin.

Share.

game da Author