Godiya Da Jinjina Ga Jama’ar Arewa, Kasancewar Su ‘Yan-Kasa-Na-Gari, Masu Kishi, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, lallai ‘yan uwana ‘yan arewa sun zama abun a yaba masu, kasancewar duniya ta shaida cewa su mutane ne masu kishin kasar su da kuma yankin su. Domin kamar yadda kuke bibiyar al’amurran yau-da-kullun, kuna sane da cewa, wasu shedanun mutane, munafukai, wawaye, jahilai, tanbadaddu, lalatattu, marasa kunya, marasa mutunci, marasa kishin kasar su da yankin su, sun dauko wata kwangila, ta yunkurin rusawa da kifar da Najeriya, su kara jefa ta cikin rudani da yake-yake, amma sai Allah cikin ikon sa, ya taimaka, ya zamanto mafi yawan ‘yan arewa, da wasu mutanen kirki daga cikin mutanen kudu, suka gano su tun da wuri, kuma suka hadu akan kunyata wadannan munafukai! Suka ki su bayar da goyon baya, domin a rusa Najeriya.

Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki, wanda ya bamu damar bayyanawa ‘yan arewa da sauran ‘yan Najeriya masu kishi cewa, wannan zanga-zangar ta #END SARS, wallahi ba komai ba ne a cikin ta illa makirci da sharri da wani yunkuri na wasu mutane, bata-gari, domin su cimma burin siyasar su ta 2023, kuma Alhamdulillahi, jama’ah sun amsa wannan kira, kuma sun amince da abun da muka fada, domin sunyi amanna cewa ba zamu yi masu karya ba, kuma ba zamu yaudare su ba, kuma ba komai muke nema akan wannan aiki ba, illa yardar Allah.

Ina mai godiya ga ‘yan uwana tare da jinjina maku akan dukkanin irin goyon baya da kuke bamu. Ina mai rokon Allah Madaukaki, ya taimake ku, kuma yayi maku sakamako da Aljannah Firdausi, amin.

Kuma wallahi, ina mai tabbatar maku da cewa, akan kare mutuncin arewa da ‘yan arewa, da kare martabar Najeriya, ko rayuwa ta a shirye nike da in sadaukar akan wannan aiki. Babu gudu, babu ja da baya, zamu ci gaba da wayar da kan ‘yan arewa, da sauran ‘yan Najeriya, har Allah yasa su shiga taitayin su, su gano irin hadarin da ke fuskantar su, daga wadannan mutane marasa kishi!

Ya ku ‘yan uwana, ku sani, wallahi ba zai yiwu ba, ya kasance kashe-kashen kabilanci, kashe-kashen ‘yan ta’addan Boko Haram, kashe-kashen barayin Shanu, talauci, yunwa, rashin aikin yi, jahilci, rashin ababen more rayuwa, rashin kulawar gwamnati da hukumomi, matsalar masu satar mutane domin biyan kudin fansa, kiyayyar juna, da hassadar juna da sauran matsalolin da suka dabaibaye yankin mu na arewa mai albarka, su ci gaba da faruwa, kuma ace muyi shiru, kar muyi magana ba! Lallai za mu ci gaba da yin magana, da wayar da kan jama’ah, tare da ci gaba da yin addu’o’i, da rokon Allah, har Allah ya dube mu da idon rahama, ya tausaya muna, ya fitar da mu daga wannan fitintinu, ta hanyar kawo muna shugaban da zai taimakawa yankin mu na arewa da Najeriya baki daya!

Don haka, wallahi, duk wani dan siyasa da baya kishin arewa da ‘yan arewa, wanda baya son ci gaban arewa, ko wanene shi, dan arewa ne ko dan kudu ne, zamu ci gaba da tona masu asiri, har sai kowa ya gane su. Babu ruwan mu da tashin hankali da fitina ko wane iri ne, kuma ko daga ina yake. Kuma bamu tare da wadannan masu zanga-zangar cin amanar kasa, da neman jefa Najeriya cikin halin damuwa. Bamu da wata kasa da ta kai matsayin Najeriya. Don haka, mun dauki alkawarin kare mutuncinta da martabarta.

Yawancin masu zanga-zangar #EndSARS kowa yasan barayi ne, ‘yan yahu-yahu, ‘yan kungiyoyin tsafi, da kungiyoyin asiri, mashaya jini. Yawancin su ‘yan luwadi ne, ‘yan madigo ne, bata-gari ne, zauna-gari-banza ne, ‘yan ta’adda ne, makiya Najeriya ne da sauran kungiyoyin ‘yan iska, wadanda basu da kyakkyawar manufa ga kasar su!

Don Allah ku dubi irin yadda wadannan miyagun, masu karyar zanga-zangar #EndSARS suka canja salon zanga-zangar zuwa tashin hankali da neman fitina da tada-zaune-tsaye!

Don haka mu har kullun muna masu gargadi ga masu wannan zanga-zangar ta shirme, da su shiga taitayin su, domin wallahi ‘yan Najeriya na kwarai, masu kishin Najeriya da gaske, ba zasu taba zuba masu ido, su bar su, suna neman su kawo rudani a kasar nan ba.

Ku kalli yadda da karfin tsiya suka shiga kurkuku a jihar Edo, suka saki fursoni da ‘yan ta’adda da dama. Kuma suka kai hare-hare daban-daban a ofishin ‘yan sanda har guda uku a jihar. A jihar Legas sun kame filin jirgin sama. Sun bude gidan rediyo, domin yada karya da yada sharrin su. Bayan haka kuma suna ta ci gaba da takura wa mutanen kasa tare da kawo rudani da tashin hankali, a Abuja da sauran wurare, wai duk da karyar suna so a kawo gyara!

Wallahi ko a jiya Litinin, na samu bayanin cewa wani daga cikin jagororin wannan zanga-zanga, wadanda suka fara da kyakyawar manufa, yace shi ya janye daga zanga-zangar, ya bar ta, saboda ya fahimci cewa wasu ‘yan ta’adda daga kasashen waje da sauran wurare daban-daban sun yi kane-kane a cikin ta. Har yake cewa ya gano wasu ne daga can suke ta turo wa masu zanga-zangar kudade domin su cigaba da zanga-zangar, ba yadda suka tsara zanga-zangar tun farko ake yin ta ba.

Haka kuma duk wasu kungiyoyi masu kyakkyawar manufa wadanda suke cikin wadanda suka shirya zanga-zangar tun farko, duk sun cire hannun su, sun janye daga zanga-zangar, saboda su ma sun gano cewa ta tashi daga matsayin da suka shirya ta.

Jama’ar kasa, masu kishin Najeriya da gaske, ma’aikata da ‘yan kasuwa da masu wasu harkoki na musamman, wallahi duk sun shiga halin ni-‘ya-su da halin damuwa a dalilin wadannan masu zanga-zangar.

Don haka yanzu abu na farko kuma muhimmi da yake wajibi, kuma tilas ga kowane dan arewa da kowa ne dan kasa nagari ya fahimta kuma ya gane, shine, kasar mu Najeriya ita ce alkiblar rayuwar mu. Abin da nike nufi a nan shi ne, duk inda kake zaune, a kasar waje kake, ko a cikin kasar nan kake, ya Allah kana cikin kauye ne ko a cikin birni, to ka sani, kai dai dan Najeriya ne, domin kuwa kana zaune ne a unguwarku, wadda ta ke karkashin karamar hukuma, sannan a karkashin jiha; wadanda su kuma baki daya suke cikin kasa mai suna Najeriya.

Kasancewar ka dan Najeriya, wallahi ba ka da wata kasa da ta kai kasar ka, don haka wajibi ne ka mayar da hankali wurin nuna kishinta da kare martabarta da mutuncinta da zaman lafiyarta. Domin kuwa idan har kasar ka ta zama mai albarka, mai daraja da martaba, to kai ne ka zama mai daraja da martaba. Idan kuma ta lalace, Allah ya kiyaye, ba fata muke yi ba, ko kuma ta balbalce, ta zama ballagaza, ta zama marar kima a idon duniya, to ka sani kai ma haka kake, kuma duk inda ka shiga a duniya, wallahi haka kowa yake kallonka, sususu, shashasha, wawa, jahili, marar hankali, marar kishin kasar sa!

Don haka idan kana so ka zama nagartacce, mai kima da martaba a kasar ka, da kuma a idon duniya, to lallai sai ka tashi tsaye, ka yi kokari iya yin ka, wurin bunkasa kasarka, da jawo mata ci gaba ta kowane fanni. Dalili na farko ke nan da yasa lallai dole ka tashi tsaye, domin ganin cewa ka zama mai kishin kasarka.

Yanzu da zamu tambayi kawunanmu, muce, ta yaya za mu zama masu kishin kasar mu Najeriya? Ta yaya kishin kasarmu zai amfane mu, kuma ya amfani al’ummar kasarmu da kuma ita kanta kasar?

Sai in ce, yana daga kishin kasa, ka kasance mai gaskiya da rikon amana a cikin dukkanin al’amuranka. Idan ka kasance mai fadin gaskiya, kuma ya zamanto kana aiwatar da al’amuranka cikin gaskiya; sannan kuma ka kasance mai rikon amana wurin mu’amalarka da mahaliccin ka, da kuma mu’amalar ka mutane, to kuwa wallahi da kasarka ta zama mai gaskiya da amana, kuma abun kauna ga dukkan al’ummomin duniya. Dalili na anan shine, a matsayinka na dan kasa, ka zama jakadanta mai gaskiya da rikon amana. Idan ka zama haka, ni ma na zama haka, wancan ma ya zama haka, ita ma waccan ta zama haka; wadancan ma suka zama haka, to shike nan an samu abin da ake nema kuma ake bukata. Ta nan ne kasarmu za ta cika da al’ummah masu gaskiya da rikon amana ke nan, wanda haka zai sanya ta zama amintacciya, nagartacciya, kuma mai aminci a cikin kawayenta na sassan duniya daban-daban.

Sannan ya ku ‘yan uwana, ku sani, kishin kasa ne ga dan kasa ya kasance mai neman na kansa, wato kada ya kasance mai zaman banza, wato wanda ba ya wani aiki ko sana’ar komai. Domin da zarar dan kasa ya zauna zaman dirshan ko zaman kashe wando, ba tare da yana wata harka ba, to wallahi babu wanda zai zame masa aboki sai shaidan la’ananne. Kuma wannan zaman banzan da yake yi zai bijiro masa da mummunan tunani daban-daban marasa kyau, sannan irin wannan tunani zai tura shi zuwa aikata munanan ayukka da ta’addanci, wadanda za su kasance halaka a gare shi, kuma su cutar da sauran al’ummar kasa. Daga nan kuma sai al’amarin ya shafi kasarsa da yankin sa, domin kuwa sunanta zai baci ta hanyar munanan ayyukan nasa.

Don haka, ya zama tilas mu tashi tsaye, mu samar wa kan mu abin yi. Kada mu ce har sai mun samu wani babban aiki ko babbar sana’a. Kuma misali, mu sani, ko da ace kayi digiri ne, ka gama jami’ah, idan ba ka samu aikin gwamnati ko na kamfani ba, to kayi kokari ka fara ko da aikin karfi ne na kwadago ko aikin hannu. Kar ka damu da dan abin da za ka samu, wallahi Allah zai iya sanya mashi albarka, kuma ka biya bukatarka, sannan ka kare mutuncinka da shi. Sannan kada ka yi mamaki, ta hanyar wannan yunkuri da ka yi na aikin karfi, Allah na iya hada ka da wata muhimmiyar sila, wadda za ta iya zama sandiyyar samun aikin da ya fi shi, domin Allah ne mai yin komai, ba karfin mu ko wayon mu ko dabarar mu ba.

Haka kuma, za ka iya fara kasuwanci, ko da da karamin jari ne. Misali, za ka iya fara sayar da katin waya. Sannu-sannu a hankali, daga ’yar ribar da za ka rika samu, matukar kana tanadi, da kadan-kadan jarinka yana iya zama mai girma. Ka sani, idan dai har ka rika gudanar da harkarka cikin gaskiya da rikon amana, tare da tsare hakkin jama’ah, kasuwancin naka yana iya bunkasa, ya zama mai albarka sosai matuka. Domin kuwa, akwai mutane da yawa da suka fara kasuwanci da karamin jari, kuma suka bunkasa har suka zama hamshakan ’yan kasuwa a yau. Misali, Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Abdus-Samad Isiyaka Rabi’u, Alhaji Dahiru Mangal, Alhaji A. A. Rano, mai kamfanin jiragen sama na Azman, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, Alhaji Muhammadu Indimi da ire-iren su, wallahi duk cikakken misali ne da kuma darasi a gare mu. Domin da za ku ji tarihin fadi-tashin su da gwagwarmayar su, da wallahi kun yi mamaki, kuma wannan zai kara sa ku ku kara yin imani da cewa Allah ne mai yi. Wadannan mutane da na lissafa maku, dukkanin su ‘yan kasuwa ne, kuma ‘yan arewa ne. Da ace sun bi hanyar cin amanar kasar su, da cutar da jama’ah ta hanyar tayar da hankula, da sunan zanga-zanga, da wallahi ba su kai matsayin da suke ba ayau.

Don haka dai, ala-ayya-halin, wallahi ya zama tilas mu san cewa, zaman kashe wando, ko zaman jiran mai yawa, wanda ko alamarsa babu, kuma babu tabbas, ba abin dogaro ba ne. Don haka, kishin kasa ne ga kowane mutum ya hana kansa zaman kashe wando, ya cire girman kai daga zuciyarsa, ya yunkura domin neman na halal komai kankantarsa.

Kishin kasa ne ga mutum ya kasance mai kaunar jama’ar sa, mai kaunar manyan sa tare da girmama su, ba tare da kuma ya nuna wariyar kabilanci ko bangaranci ko babbancin addini ba. Kada ka ce za ka yi mu’amala ne kawai da ’yan kabilarka, ko kuma ka ce ’yan kabilarka ne kawai mutanen kirki, don haka babu ruwanka da wasu kabilu. Idan ka yi haka, babu shakka ba ka nema wa kasarka da yankin ka alheri ba, kuma ba ka zama mai kishinta ba. A lokacin da ka dauki ’yan kabilarka kawai a matsayin mutane, ka wulakantar da sauran jama’ah, mutanen kirki, kawai domin su ba naka ba ne, to lallai akwai matsala. Na farko dai, kai kanka za ka gamu da matsala, domin kuwa al’ummar kasarka sun kasance kabilu daban-daban ne, masu yare daban-daban ne, masu al’adu daban-daban ne, sannan kuma ya zama wajibi, dole su yi rayuwa tare da wasu kabilun, tun da duk ’yan Najeriya ne, babu mai iya korar wani daga Najeriya. Wata rana, dole ne za ka nemi wata bukata, wadda dan kabilarka ba zai iya biya maka ita ba. Idan haka ta kasance, to yaya za ka yi kenan, tunda ba ka dauke su a bakin komai ba?

Amma abun da muke cewa, kuma muke kira akai, kuma muke son kowane dan arewa ya sani, shine, lallai wanda kawai zamu so, kuma mu goya wa baya, shine mai son arewa da ‘yan arewa. Mai kishin arewa da ci gaban arewa. Kuma ko dan arewa ne ko ba dan arewa ba. Amma duk wani makiyin arewa da ‘yan arewa, wallahi bamu son shi, kuma wallahi zamu ci gaba da yakar sa ta kowa ne hali. Wannan shine manufar mu!

Daga karshe, ina kira, mu sani, ya zama tilas, dole, kuma wajibi a gare mu da mu zama masu kishin yankin mu na arewa, masu kishin kasa, masu kishin jama’ar mu da dukkanin ‘yan Najeriya masu kishi, kuma masu kyakkyawar manufa gare mu, da yankin mu, da kuma kasar baki daya, domin ta haka ne su ma yaran mu kanana, masu tasowa za su taso da kishin kasar su Najeriya.

Sannan ya zama tilas muyi taka-tsan-tsan, muyi hankali da wadannan masu zanga-zangar, ‘yan-bani-na-iya, marasa kunya, kuma marasa kishin kasa, domin akwai karancin gaskiya, da karancin rikon amana, da rashin son hadin kai da kuma rashin kishin kasa, da rashin son zama lafiya a cikin zukatan su. Domin in dai har zasu samu kudi, in dai har aljihun su zai cika, ku su ji alat a cikin asusun ajiyar su na banki, to ko iyayen su suna iya sayarwa, kuma wallahi basu ki kasar nan ta fada cikin tashin hankali da fitina da yake-yake ba. Wannan shine manufar su, mu kula!

Matasan arewa masu albarka, ina kiran ku, ku sani, wallahi so ake yi ku shiga cikin wannan zanga-zangar ta sharri, domin ku karasa rusa dan abun da ya rage, kuma yayi saura a yankin ku. Kar ku yarda da su, kar ku saurare su. Kar ku yarda a karasa ku. Har kullun, kuyi kokarin ganin cewa Allah ya kawo maku zaman lafiya a yankin ku!

Daga karshen makala ta, zan rufe da fassarar taken kasar mu Najeriya, domin mu kara sanin me ya kunsa, kuma mu kara son kasar mu. Ga shi kamar haka:

Yaku ‘yan Najeriya ku farka;
Ku amsa kiran Najeriya;
Domin mu taimaki kasarmu ta haihuwa;
Don aiki ga kasata cikin soyayya da rikon gaskiya;
Domin gudummawar da shuwagabaninmu ‘yan kishin kasa suka bada;
kada ta zama a banza;
Muyi aiki da zuciya daya da girmamawa a gare ta;
Domin ta kasance kasa daya mai ‘yanci ga kowa tare da hadin
kai da zaman lafiya.

Alkawali ga Kasa ta Najeriya:

Na dau alkawali ga kasata;
Zan zama mai mutunta ta, mai biyayya da gaskiya;
Zan yi amfani da duk karfina wurin bauta mata (ma’ana: zan yi aiki domin zaman lafiyar ta da ci gaban ta da dorewar ta);
Zan tabbatar da hadin kanta, da kokarin rike mutuncin ta don ganin daukakar ta;
Allah ya taimake ni;
Amin!

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta wannan daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author