Har kara na an kai wajen Buhari wai, nine nake ingiza mutane su yi bore a Legas – Inji Tinubu

0

Jagoran jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya ce yayi amanna cewa ba Buhari bane ya sa a bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki, jihar Legas ba.

Tinubu ya bayyana cewa, kamar yadda wasu ke zargin wai shine ya sa aka bude wa masu zanga-zangar #EndSARS wuta a Lekki, haka kuma wasu suka kai karar sa fadar shugaban kasa wai gashi can ya ingiza matasa suna wa gwamnati bore.

” Ko a lokacin da na ji an bude wasu zanga-zanga wuta, na yi kokarin kiran babban hafsan tsaron kasa, da maiba shugaba Buhari shawara kan harkar tsaro, ban same su. Dama kuma ba a kiran shugaban kasa a irin wannan lokaci.

” Bai kamata ace an yi amfani da harsasan gaske ba, na roba ake amfani da su wajen yarwatsa masu zanga-zanga.

Sannan kuma Tinubu ya yi bayanin korafin da ake yi wai shine ke da mallakin wannan mashiga ta Lekki, inda ya ce ba shine mai mallakin wannan mashiga ba.

EndSARS: Buhari ya roki masu zanga-zanga su yi hakuri, su yayyafa wa zuciya ruwan sanyi

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki a zauna lafiya, hakuri da kuma kai zuciya nesa. Kiran na ya zo ne kwana daya bayan sojoji sun bude wa masu zanga-zanga wuta, sun kashe wasu a Lekki, cikin Lagos.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos, ya ce wadanda su ka yi kisan wasu ne da sun fi karfin tsawatarwar gwamnatin sa.

Ya ce gwamnatin jihar sa ba ta da iznin sa sojoji su yi ko su bari. Ya dora laifin a kan gwamnatin tarayya.

Sojoji a karkashin shugaban kasa su ke, kuma shi ne Babban Kwamandan Askarawan Najeriya. Wato kenan babu mai iya bada iznin a bude wuta sai Shugaba Buhari.

Cikin wata sanarwa da kakakin sa Femi Adesina ya sa wa hannu, Buhari ya roki a yi hakuri, a kai zuciya nesa, sannan kuma a guji tarzoma.

Sai dai har a karshen bayanin babu inda ya yi maganar kisan da sojoji su ka yi a Lekki.

Daga nan ya jaddada aiwatar da canje-canje a hukumar ‘yan sanda da kuma aiwatar da dukkan kudirorin da Kwamitin Shugaban Kasa kan SARS ya ce a zartas.

Ana ta kiraye-kirayen Buhari ya fito ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi dangane da halin da ake ciki.

Zanga-zangar da aka fara kwanaki biyu domin neman a rushe SARS, tuni ta rikide ta koma mummunar tarzoma, musamman a Lagos, inda ake ci gaba da kona kadarori da hukumomin gwamnatin tarayya da na jihar Lagos da kuma na jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Share.

game da Author