Kungiyar mai zaman kanta ‘RBM Partnership to End Malaria’ ta bayyana cewa ta ci gaba da daukan matakan dakile yaduwar zazzabin cizon sauro a Afrika, Asia da Amurka.
Kungiyar ta ce a yanzu haka matakan da suka dauka ya kai kashe 90 bisa 100 duk da fama da aka yi da annobar Korona na tsawon lokaci kuma har yanzu ana fama dashi.
Kungiyar ta fadi haka ne a wani takarda da ta aika wa PREMIUMTIMES.
Zuwa yanzu kasashen dake kokarin ganin sun rabu da zazzabin cizon sauro kwata-kwata sun kara zage damtse domin ganin burin su ya cika.
Zazzabin cizon sauro cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cizon sauro.
Alamun ta sun hada da zazzabi, ciwon Kai, rashin iya cin abinci, ciwon gabobin jiki da sauran su.
Cutar na iya yin ajalin mutum Idan ba a gaggauta Neman maganin ba.
Kungiyar ‘RBM Partnership to End Malaria’ na daya daga cikin kungiyoyin dake yaki da cutar zazzabin cizon sauro a duniya.
Yaduwar cutar
Idan ba a manta ba a watan Afrilu ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa bullowar cutar korona zai sa a samu karuwa a yaduwar zazzabin cizon sauro da yawan mutanen da za su mutu a dalilin cutar.
WHO ta ce za a fada wannan matsala ne saboda rashin maida hankali wajen kawar da zazzabin cizon sauro da za a yi saboda bullowar cutar korona.
Matakan kawar da cutar da kungiyar ta dauka
Kungiyar RBM Partnership to End Malaria’ ta bayyana cewa kamata ya yi a maida hankali wajen kare mata da yara kanana daga kamuwa da zazzabin cizon sauro.
Kungiyar ta ce kare kiwon lafiyar mata musamman masu ciki zai taimaka wajen kawar da matsalar haihuwan yara da matsaloli.
Bayan haka jami’ar ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Mali, Aminata Traore ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da su samar da isassun magungunan kawar da cutar zazzabin cizon sauro musamman ga mata masu ciki domin kare kiwon lafiyar su.