A ranar Litini ne wasu mahara dauke da makamai suka far wa kauyen Wereng dake karamar hukumar Riyom jihar Filato inda a nan saka kashe dagacin kauyen da wasu mutane biyar.
An gano cewa yariman garin da wasu mutum uku ‘yan gida daya na daga cikin mutanen da aka kashe a wannan hari.
Sannan kuma an harbi wani Francis a kafa, David da Mary an harbe su a cinyoyin su.
Idan ba a manta ba makonni biyu da suka gabata ne PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda mahara suka kashe dagacin kauyen Foron a karamar hukumar Barakin Ladi sannan suka kashe wasu mutane a kauyen Vwang dake karkashin karamar hukumar Jos ta Kudu.
Sannan jaridar ta ruwaito yadda wasu maharan suka kashe wani ma’aikacin jami’an tsaro na SSS Muktar Modibbo yayin da jami’an tsaron suka kai wa maharan harin ba zata wani maboyar su dake karamar hukumar Shendam.
Da yake ganawa da manema labarai kwamishinan ‘yan sanda Edward Egbuka ya nuna bacin ransa kan wannan harin da aka kai yana mai cewa hakan ya auku ne a daidai ana ci gaba da zaman tattauna samar da zaman lafiya a yankin da rundunar tsaro ke yi da mutanen yankin.
Bayan haka gwamnan jihar Simon Lalong ya bada umurnin a kamo duk wadanda ke da hannu a tada rikicin da ake fama da shi a yankin.
Lalong ya yi kira ga jami’an tsaro su ba himma wajen ganin sun kamo masu tada zaune tsaye a yankin.
Discussion about this post