ZABEN EDO: Yau Fa Za A Yi Ta Ta Kare!

0

Ranar da ake ta jira domin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, wato 19 Ga Satumba, ta zo, kuma tun da jijjifin safiya harkokin matakan gudanar da zabe ke ta kankama a mazabu da rumfunan zaben fadin jihar.

Duk da cewa jam’iyyu 14 ne su ka shiga takara, tabbas za a iya cewa wannan zabe takara ce tsakanin jam’iyyar PDP da APC kawai, sauran jam’iyyu 12 duk ‘yan rakiyar-amarya ne.

Yayin da PDP ta tsaida Gwamna Godwin Obaseki, ita kuwa APC Ize-Iyamu ta tsaida. Masu nazari na ganin zaben zai yi zafi sosai, domin dukkan ‘yan takarar biyu na takama da dimbin ‘sinadaran’ da ake bukata a ci zabe a Najeriya.

Ya zuwa ranar zabe Asabar din nan, duk wani katakoro ko gazaguru da gogarman siyasar da APC da PDP ke takama da shi, ya na can a Jihar Edo, domin taimaka wa dan takarar bangaren sa yadda zai yi nasara a wanan ‘fadan karshe’, wanda shi ne za a yi ta ta kare.

PREMIUM TIMES HAUSA ma ba a bar ta a baya ba, domin ta hada guiwa da PREMIUM TIMES da kuma bangaren Masu Binciken Kwakwaf na Aikin Jarida a PREMIUM TIMES (PTCIJ), sun baza wakilan su birjik a jihar domin dauko wa masu irin rahoton da mu ka saba daukowa, wanda ya sa mu ka ci sunan mu na “Ba A Ba Mu Labari, Sai Dai Mu Bayar.”

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar da zaben a Kananan Hukumomi 18, Mazabu 192 da Rumfunan Zabe 2,672.

Mutum 2,210,534 ne su ke da rajistar zabe a jihar. Amma mutum 1,726,738 ne su ka karbi katin shaidar rajistar zabe. Don haka wannan adadin ne kadai za su yi zabe a wannan rana, ku ma su ne za su fito da wanda zai yi nasara a tsakanin Godwin Obaseki ko kuma Ize-Iyamu.

Ku biyo mu kai-tsaye ku rika ganin abin da ke faruwa, daga nan har lokacin da INEC za ta bayyana sunan wanda ya yi nasara da wanda ya ci kubeji.

Share.

game da Author