Mashawarcin Gwamna Obaseki a Bangaren Yada Labarai, Crusoe Osagie, ya zargi wasu jami’an Hukumar Zabe ta Kasa, INEC da baddala zaben, wanda ake kan gudanarwa a Jihar Edo.
Cikin wata sanarwa da ya turo wa PREMIUM TIMES, Osagie ya nuna takaicin yadda ya ce aka rika baddala zabe, a yankunan da Gwamna Obaseki ke da rinjaye.
“Ba zato ba tsammani sai mu ka ga ‘Card Readers’ sun daina amfani, a yankunan da Obaseki ke da dimbin magoya baya.
Ya ce “ana danne wa masu zabe hakki da ‘yancin su na jefa kuri’a. Tilas mu fito mu bayyana cewa wannan abin zagon-kasa ne shiryaoe.”
” Mun ga abin da ya faru a Oredo Mazaba ta 1, Rumfa ta 29 da sauran wurare da dama, inda gwamna ke da rinjayen magoya baya, duk sai na’urar tantance masu zabe (card readers) su ka ki aiki.
“Ya zama wajibi Hukumar Zabe ta Kasa ta nuna wa al’ummar Jihar Edo cewa za a iya yi masu sahihin zabe kuma karbabbe.” Inji shi.
Ma’aikatan Premium Times da ke wuraren zaben na can na tantance gaskiya ko akasin wannan zargi.
A ranar Juma’a, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, ya gargadi jami’an zaben da ke gudanar da zabe a jihar Edo cewa su tabbatar ba su goyi bayan wata jam’iyya ko wani dan takara ba.
Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargadi ma’aikatan zabe gaba daya cewa kada su kuskura su nuna fifiko ga wata jam’iyya ko wani dan takara a zaben gwamnan Jihar Edo da za a fara kada kuri’a safiyar nan.
Wannan gargadi ya fito ne kwana daya kafin fara jefa kuri’a, a zaben wanda kusan a kan sa an sa wa Najeriya ido, domin ganin yadda za a wanye.
Shi ma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa kada ‘yan siyasa su maida zaben ‘a-ci-ko-a-mutu.’
Shugaban na INEC, ya kara da cewa, “a yayin da mu ke kan gangara zuwa ranar da za a yi zaben gwamna na Jihar Edo, a bayyane ta ke cewa yanzu kowa ya maida hankalin sa kan yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar da zaben cikin lumana da adalci kuma ta hanya mai inganci.
“Ba ni da haufi ko kadan cewa ma’aikatan mu za su ba marada kunya. Mun yi irin wannan aikin cikin nasara a da, kuma za mu sake yin irin sa yanzu din ma. Hukumar ta na bayyana gamsuwar ta da irin sadaukar da kai ba tare da gajiyawa ba da ma’aikatan mu ke yi a ko da yaushe, sau da yawa ma har a lokacin da ba na aikin su ba, don tabbatar da mun sauke nauyin da aka dora mana.
“Shugabannin hukumar za su ci gaba da kokari wajen inganta hakkokin ma’aikatan mu don kara masu kwarin gwiwa a cikin halin da ta ke da shi.
“Zan yi amfani da wannan dama in yi kira a gare ku da ku ci gaba da jajircewa tare da yin tsayin daka kan akidojin hukumar. ‘Yan Nijeriya da kasashen waje sun sa ido su ga yadda za ku sauke nauyin mu. Sun zura mana ido. Ya na da muhimmanci duk mu tsare gaskiya a aikin mu.
“Tilas ne mu tabbatar da cewa ba mu bada fifiko ga wata jam’iyya ko dan takara a kan wani ba. Tilas ne mu tsaya a matsayin alkalai ‘yan ba-ruwan mu, kuma mu tsare Ka’idojin Aiki da Rantsuwar Rashin Nuna Wariya wadanda duk mun yi amanna da su.
“Domin kuwa, a karshe, zai kasance dukkan mu mun bada gudunmuwa ga dorewar mulkin dimokiradiyya da ingantaccen tsarin gudanar da zabe wanda duk ‘yan Nijeriya za su iya amincewa da shi.
Na gode da dukkan ƙoƙarin ku.”