ZABEN EDO: Obaseki da magoya bayan sa sun rika binciken motoci domin hana sayen kuri’u

0

An nuno bidiyon yadda Gwamna Godwin Obaseki da wasu magoya bayan sa su ka rika tare motoci, su na binciken yiwuwar sayen kuri’u.

Hakan ya faru ne a wurin da aka rika ajiye motoci a rumfar zaben da Obaseki ya jefa kuri’a.

PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda Obaseki da matar sa su ka jefa kuri’a a Runfar Zaben da ke Mazabar Firamare ta Emokpae, 004, cikin Karamar Hukumar Oredo

Bayan ya jefa kuri’a, ya ja zugar matasan sa masu yi masa kirakin 4+4, su ka rika binciken motocin da aka yi fakin a filin makarantar da ya jefa kuri’a.

Hakan ya biyo zargin cewa akwai ‘yan adawa sun je da buhunan kudi domin sayen kuri’u a mazabar gwamnan.

Obaseki na neman zarcewa ne zango na biyu a karkashin PDP, bayan da ya shafe shekara hudu ya na gwamna a karkashin APC.

Dangane da yadda zaben ke gudana, PREMIUM TIMES ta tura wakilai da dama a Jihar Edo, masu dauko mata bayanan yadda zaben ke gudana.

Share.

game da Author