Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya jefa kuri’a wajen karfe 10:55 na safe, a Rumfar Zaben Mazaba ta 10, ta Arewacin Uzairue, Etsako ta Yamma kenan.
Sai dai kuma bayan ya kammala jefa kuri’a, Oshiomhole wanda ya yi gwamnan Edo tsawon shekaru takwas, ya yi korafi dangane da wasu jami”an INEC duk da dai ya ce ya gamsu da yadda zabe ke gudana.
“INEC ce kadai batagari a wannan zabe, saboda yawancin na’urorin tantance masu jefa kuri’a (Card Readers) duk ba su aiki.” Inji Oshiomhole.
Ya ce wannan tsaiko da card readers su ka kawo, gaskiya ya na rage wa tafiyar da zaben tafiya yadda ya kamata kan hanyar da ta dace.
Oshiomhole ya jinjina wa jami’an tsaro da kuma masu jefa kuri’a, saboda a cewar sa, sun nuna nstsuwa wajen kula da yadda ake jefa kuri’a.
Ya kuma ja kunnen jami’an tsaro su kara kula sosai kada ‘yan jagaliyar siyasa su hargitsa rumfunan jefa kuri’a
Oshiomhole ya yi mulkin Edo daga 2008 zuwa 2016. Ya fara a karkashin jam’iyyar AC, wadda a karkashin ta ne ta koma ACN daga nan kuma aka hada jam’iyyar APC.
A wannan zabe dai Cibiyar Zakulo Labaran Kwakwaf ta PREMIUM TIMES (PTCIJ) ta tura ‘yan sa-ido 54.
Baya ga wakilai masu yawa da jaridar PREMIUM TIMES ta turo domin dauko labaran yadda ta kwaranye a zaben gwamnan jihar Edo, bangaren Cibiyar Zakulo Labaran Kwakwaf ta PREMIUM TIMES ya tura ‘yan-sa-ido har mutum 54.
An dora musu alhakin dauko rahotannin duk wani abin da aka aikata na ba daidai ba, kama daga bangaren jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, jami’an zabe da kuma jami’an gwamnatin jiha ko na tarayya, wadanda su ka yi duk wani kokarin kawo kafar-ungulu wsjen tabbatar da an gudanar da sahihin zabe.
An raba mutum uku a kowace Karamar Hukuma, daga cikin Kananan Hukumomi 18 na Jihar Edo.
Daraktan cibiyar ta PTCIJ, Tosin Alagbe ya roki al’ummar jihar Edo su yi zabe lami lafiya, su ba marada kunya, masu kallon cewa ba zabe za a yi a Edo ba, gangamin zubar da jini ne kawai za a yi.
Tuni dai aka fara jefa kuri’a a wasu mazabu da rumfunan zabe. Daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, dan takarar APC, Ize-Iyamu ya jefa kuri’a.
Shi ma tsohon gwamnan jihar, kuma saukakken shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole an gan shi tsaye a kan layin jefa kuri’a.
An samu rahoton cewa a wasu kananan hukumomi masu jefa kuri’a da da jami’an zabe, ba su bi umarnin da Hukumar Dakile Cutar Korona (NCDC) ta bayar cewa jama’a su tsaya nesa da juna tazarar mita biyu tsakani ba.