Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ta kammala duk wani shiri da tsari da ake buƙata don tabbatar da an yi zaben gwamnan Jihar Edo cikin nasara a ranar Asabar din nan.
Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a Abuja.
Okoye ya ce INEC ta gama shirya wa zaɓen tsaf.
Ya ce duk wasu kayan aiki marasa hadari da aka tanadar don zaben na Edo an gama kai su cibiyoyin zaɓe tun cikin Agusta.
“ Kayan aiki masu hatsari, wato irin su fom-fom na rubuta sakamakon zabe da kuma takardun kuri’u, wadannan sun isa Jihar Edo ne a ranar Litinin ” inji shi.
“Jiya (Laraba), an yi taro da dukkan jam’iyyun siyasa kan yadda za a duba yadda ake gudanar da zaben.
“Su kayan aikin sun bar harabar Babban Bankin Najeriya ne a yau din nan (17 ga Satumba) zuwa dukkan kananan hukumomi, kuma waɗannan kayan an rarraba su ne bisa tsarin wuraren da aka yi rajista.
“Mu na da wuraren da aka yi rajista guda 192 a Jihar Edo ko kuma abin da za ka kira unguwanni. Saboda haka, an rarraba wadannan kayan aiki a bisa tsarin unguwannin, sannan kuma dukkan kuri’un da fom-fom da za a rubuta sakamako an yi masu kalolin da kowacce ta dace da ƙaramar hukumar ta.”
Okoye ya kara da cewa hukumar ta kuma yi wani tsari na sufuri don magance matsalar samun tsaiko wajen kai kayan aiki zuwa cibiyoyin zake a ranar zaɓe.
Ya bayyana cewa tunda INEC ba ta da wadatattun motoci da za su yi aiki a ranar zaken, ta kan ɗauko hayar motoci ne daga kungiyar ‘yan yuniyan (NURTW) da ƙungiyar mamallaka motocin haya, wato NARTO, kuma kowacce an ɗau bayanin ta.
Sai dai Okoye ya lura da cewa wasu daga cikin su ba a ganin su a ranar zaɓen duk da yake an biya su rabin kuɗin jingar da aka yi da su.
Ya ce, “Abin da mu ka yi shi ne mun tura motocin mu ƙirar Hilux daga jihohi makwabta waɗanda su ba su da zabe a ranar, saboda mu yi amfani da su idan an samu matsala irin wannan.
“Na biyu, akwai wasu ƙananan hukumomi kalilan waɗanda ke cikin yankin ruwa a Jihar Edo. Don haka mun tuntubi rundunar ‘yan sandan ruwa da ta sojan ruwa, waɗmdanda za su samar da jiragen yaƙin ruwa don kare wasu ma’aikatan mu da za su yi aiki a waɗannan yankunan.
“Mu na aiki tukuru don tabbatar da cewa ba mu da irin wannan matsalar wajen raba kayan aiki a ranar zaben.’’
Okoye ya kara da cewa hukumar ta kammala horas da dukkan ma’aikatan ta na zabe, yayin da horaswa domin tattara sakamako daga unguwanni da ƙananan hukumomi da na jiha, wanda a kan bar shi har sai ya rage biyu kafin ranar zabe, shi ake gudanarwa a yanzu.
Bugu da kari, ya ce babu malamin zabe ko ɗaya da aka ɗauka daga kowace babbar makaranta da ke cikin Jihar Edo, sai dai wadanda ke wajen jihar.
Ya ce, “Saboda haka a game da wannan zaben, hukumar ta gama shirya komai. Mun kammala dukkan tsare-tsare da abubuwan da za a yi don gudanar da wannan zaben.
“Kamar yadda ku ka sani, mun tura Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe (Resident Electoral Commissioners, RECs) guda biyar don su bada gudunmawa ga shi kwamishinan zabe da ke Edo. Kuma mun tura manyan kwamishinoni na kasa (National Commissioners) guda uku domin su ma su je su bada tasu gudunmawar. Saboda haka mun shirya tsaf.”
Discussion about this post