Rikicin APC ya kazanta a Ekiti, An dakatar da gwamna Fayemi daga Jam’iyyar

0

Rikicin da ya barke a tsakanin bangarorin da basu ga maciji a tsakanin su, kuma ƴaƴan jam’iyyar APC, a jihar Ekiti ya daɗa kazanta.

Bangaren Jam’iyyar ta dakatar da gwamnan jihar daga Kayode Fayemi daga jam’iyyar.

Idan ba a manta ba, dama bangaren jam’iyyar a ranar Laraba ta dakatar da maiba shugaba Buhari shawara, Babafemi Ojudu da wasu mutum 10 daga Jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce an dakatar da wadannan ƴaƴan jam’iyya ne a bisa dalilin kin bin umarnin jam’iyya na janye duk wata shari’a dake kotu kan APC.

Shugaban bangaren jam’iyyar da ta dakatar da gwamna Fayemi, Tony Adeniyi, ya bayyana cewa tuni sun banƙaɗo ƙulle ƙulle da zagon ƙasa da gwamna Fayemi yake wa jam’iyyar domin cika burinsa na zama mataimaki shugaban kasa da kuma aiki da yake yi wa PDP a ɓoye.

Idan ba a manta gwamna Fayemi har jihar Ribas ya taba tafiya dubban n kaddamar da ayyukan gwamnatin PDP dake mulki a jihar. Sannan kuma mun ga yadda hadiman sa a fadar gwamnatin jihar ke bukin kada APC da aka yi a jihar Edo.

Ana zargin Fayemi da hada kai da PDP, domin samun damar takarar kujerar mataimakin shugaban Kasa idan bai samu ba zama dan takarar shugaban kasa a APC ba.

APC a jihar Ekiti dai ta fada cikin cakwakiyar siyasar cikin gida da ya ke neman ya rusa jam’iyyar bayyan rarraba kawunan ƴaƴan ta.

Share.

game da Author