SARAUTAR ZAZZAU: Babu sunan Magajin Gari Ahmadu Bamalli cikin sunayen da aka aika wa gwamna El-Rufai

0

Iyan Zazzau, Bashar Aminu, ne ya samu mafiyawan maki cikin sunayen da aka mika wa gwamnan jihar Kaduna domin zaben daya daga cikin su ya zama sarkin Zazzau din.

Wanda da yawa ake ganin zai iya zama sarki kuma makusancin gwamnan Kaduna, Ahmed Bamalli bai ma samu dacewa an zabe shi cikin jerin wadanda aka mika wa gwamnan ba.

Iya Bashar Aminu daga gidan Katsinawa, ne ya samu maki da ya fi yawa, ya samu maki 89%, sai Yeriman Zazzau da ya samu maki 87%, sai Turakin Zazzau Aminu Ideis dake da maki 53%.

Cikin masu zaben sabon sarki, uku sun zabi Iya Bashar, shi kuma Yerima da Turaki sun samu ƙuri’a daidai.

Idan har Iya ya samu kujerar sarautar Zazzau, gudan Katsinawa za su ci gaba da sarautar ke nan fiye da shekara 61 a kasar Zazzau.

Wani abinda da ya daure wa mutane kai shine wancakalar da sunan Magajin Garin Zazzau da masu zaben sabon sarki suka yi.

Duk da cewa ana ganin kusancin sa da gwamna, sai gashi tun daga gida basu yarda masa ba.

Sai dai ba anan gizo ke sakar ba, domin koma waye aka tsayar, sai wanda gwamna ya ga yafi dacewa da salon mulki na zamani da kuma wanda ya kwanta masa, domin shine wuka shine nama.

Tuni dai an ce gwamna El-Rufai ya kira kwamitin tsaro na jihar tun da safiyar Juma’a domin su kinkintsa da shirin kobta kwana.

Share.

game da Author