Majalisar Dinkin Duniya ta jawo hankalin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin Jihohi cewa su tabbatar sun fara dauka da tanadar dukkan matakan kariya daga cutar Korona, kafin a maida dalibai makarantu tukunna.
UN ta ce akalla akwai daliban firamare da na sakandare kimanin su milyan 46 a Najeriya, wadanda kulle makarantu ya shafe su, suka koma su na zaman gida tsawon watanni shida kenan.
Rasdan na UN a Najeriya, kuma Kodinetan Kula Da Ayyukan Jinkai, Edward Kallon ne ya bayyana haka a ranar Lininin, yayin da ya yi jawabi a wurin Ranar Kare Ilmi ta Duniya.
Sunan taron, “Kare Yara, Kare Al’umma Ce.” An gudanar da shi ne a Abuja.
Tuni dai wasu jihohi suka fara bayyana ranakun da za su koma makarantun sakandare da firamare.
Sai dai kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASSU) ta ce ba za ta koma koyar da dalibai a jami’o’in kasar nan ba, har sai nan tabbatar da an samar da dukkan kayan da suka wajaba a yi amfani da su a makarantun wajen kauce wa kamuwa da cutar Korona.
Shugaban ASSU, Ayo Akinwole, ya ce ko wasu dalibai sun koma makaranta, to jami’o’i ba za su koma ba, har sai sun wadatu da kayan kariya daga cuta a kowace makaranta.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda daliban sakandare masu fita da suka rubuta jarabawar WAEC kwanan nan, an samu 20 a cikin su da suka kamu da cutar Korona a Jihar Bayelsa.
Kallon ya kuma tuna yadda ‘yan bindiga suka sace dalibai bakwai da malamin su, a lokacin rubuta jarabawar WAEC, a kauyen Damba-Sakaya, Karamar Hukumar Chikun, Jihar Kaduna.
A ranar Laraba kuma Kungiyar Malaman Kwalejojin Ilmi sun ce kwalejojin ba su shirya komawar dalibai ba tukunna.