Gwamnatin Tarayya ta tsame hannun ta daga yanka farashin litar man fetur a Najeriya, ta na mai cewa daga yanzu kowane dillalin ferur zai iya saidawa a farashin da ya ga zai iya cin riba kawai.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Hukumar Kayyade Farashin Fetur da Gas ta Kasa (PPPRA).
“Daga yanzu babu sauran kayyade farashi, kowane dillalin mai ya fita ya samo mai duk inda zai iya sayowa. Kuma ya saida man sa a farashin da ya yi masa daidai.
“Gwamnati ta tsame hannun ta a sha’anin kayyade farashin litar fetur a kasar nan. Amma za ta rika sa-ido domin tabbatar da cewa masu gidajen mai ba su wuce-gona-da-iri ba”
A ranar Talata PPPRA ta bayyana tsame hannun ta daga kayyade farashin litar man fetur, kamar yadda dama Karamin Ministan Fetur, Timipre Sylva ya taba fada cikin watan Afrilu cewa gwamnati za ta janye hannun ta daga kayyade farashin litar fetur.
Babban Sakataren Hukumar Kayyade Farashin Fetur, Abdullahi Sa’idu ne ya bayyana janye hannun hukumar daga kayyade farashin litar fetur.
Wanann katankatana ta taso tun cikin watan Maris lokacin da farashin danyen mai ya karye a kasuwar duniya, Najeriya ta rasa isassun kudaden shiga.
Farkon Satumba gwamnati ta janye tallafin fetur, wanda a sanadiyyar haka litar fetur ta karu.
Karin kudin fetur ya zo daidai da karin kudin wutar lantarki da kuma yanayi na masifar tsadar rayuwar da ta haddasa tsadar kayan abinci.
Yayin da ake tsakiyar caccakar gwamnatin Buhari, ya fito ya ce karin kudin fetur ya zauna daram, domin idan ba a kara kudin ba, to saboda karancin kudaden shiga, Najeriya za ta iya shiga mawuyacin hali.
Tuni dai a wasu jihohi aka fara zanga-zangar rashin amincewa da karin kudin fetur da na wutar lantarki.
Kungiyoyin kwadago da na dalibai da sauran jama’a na ta kiraye-kirayen cewa ba za su amince da karin kudin ba.
Shugaba Buhari ya hau mulki bayan ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin za a rika sayen litar fetur naira 45 a maimakon naira 89 da ta ke a lokacin, karkashin mulkin Jonathan.
Sai dai kuma tun bai yi nisa ba aka yi wani mahaukacin karin kudin litar fetur zuwa naira 145.