Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 176 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 34, FCT-40, Filato-26, Enugu-14, Delta-12, Ogun-12, Ondo-9, Oyo-8, Ekiti-6, Ebonyi-4, Adamawa-2, Nasarawa-2, Kwara-2, Rivers-2, Edo-1, Osun-1 da Bauchi-1
Yanzu mutum 55,632 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 43,610 sun warke, 1,070 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 10,952 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,456 FCT –5,375, Oyo – 3,209, Edo –2,603, Delta –1,780, Rivers 2,195, Kano –1,728, Ogun – 1,715, Kaduna –2,214 Katsina -819, Ondo –1,575, Borno –741, Gombe – 746, Bauchi – 671, Ebonyi – 1,034, Filato -2,954, Enugu – 1,198, Abia – 816, Imo – 537, Jigawa – 322, Kwara – 989, Bayelsa – 391, Nasarawa – 443, Osun – 803, Sokoto – 159, Niger – 244, Akwa Ibom – 283, Benue – 640, Adamawa – 230, Anambra – 226, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 299, Taraba- 91, Kogi – 5, da Cross Rivers – 83.
Masana kimiya za su fitar da maganin korona dake da inganci.
Masana kimiya dake aiki da kamfanonin sarrafa magunguna guda Tara sun yi alkawarin hadawa da samar da maganin rigakafin cutar korona da suka tabbatar da inganci da sahihancin sa.
Wadannan kamfanoni guda tara sun hada da AstraZeneca, BioNTech, GlaxoSmithKline, Johnson & Johnson, Merck, Moderna, Novavax, Pfizer da Sanofi.
Kamfanonin sun ce yanzu da duniya ta matsu a samar da maganin rigakafin cutar korona sun ce za su fitwr da maganin rigakafin ne bayan sun gudanar da gwaje-gwaje bisa ga sharuddan kimiya domin ganin maganin bai cutar da kiwon lafiyar mutane ba.