Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 187 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –74, Filato-25, Rivers-25, Gombe-19, FCT-19, Osun-10, Kaduna-5, Borno-3, Ogun-2, Katsina-2, Nasarawa-1, Bayelsa-1 da Edo
Yanzu mutum 58,647 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 49,937 sun warke, 1,111 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,599 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,384, FCT –5,696, Oyo – 3,260, Edo –2,626, Delta –1,802, Rivers 2,395, Kano –1,737, Ogun – 1,838, Kaduna –2,407, Katsina -861, Ondo –1,631, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 699, Ebonyi –1,040, Filato -3,425, Enugu – 1,289, Abia – 894, Imo – 568, Jigawa – 325, Kwara – 1,034, Bayelsa – 399, Nasarawa – 450, Osun –837, Sokoto – 162, Niger – 259, Akwa Ibom – 288, Benue – 481, Adamawa – 234, Anambra – 237, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 76, Ekiti – 321, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Korona ta kashe mutum miliyan daya a duniya
Sakamakon rahoton ‘Wordometer’ ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar korona ya kashe a duniya ya kai miliyan daya.
A lissafe dai bisa ga rahoton mutum 1,000,502 ne suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar.
Mutum 209,000 ne suka mutu a kasar Amurka, kasar Indiya dake bi mata nada mutum 95,000 da suka mutu.
Zuwa yanzu adadin yawan mutanen da Suka kamu da cutar a duniya ya kai mutum miliyan 33.
Duk da haka wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce akwai yiwuwar mutanen da suka kamu da cutar da wadanda cutar ta kashe basu a cikin lissafi saboda rashin bincike.
Ranar Asabar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar cutar za ta kashe mutum miliyan 2 kafin a gano rigakafin ta.
Zuwa yanzu mutum miliyan 24 sun warke daga cutar a duniya.
Nahiyar Afrika
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC ta bayyana cewa cutar korona ta kashe mutum 35,000 a Afrika.
Zuwa yanzu mutum miliyan 1.4 ne suka kamu da cutar a Afrika.
Kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun ce rashin yin gwajin cutar ne yake sa ba a iya tabbatar da adadin yawan wadanda suka kamu da wadanda suka mutu a Nahiyar ta Afrika.
A Najeriya mutum 58,324 suka kamu da cutar, 49,794 sun warke, 1,108 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,422 ke dauke da cutar.
Discussion about this post