KORONA: A dan dakata da bude makarantu tukunna – Boss Mustapha ga Gwamnoni

0

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan daƙile yaɗuwar Korona, Boss Mustapha ya gargaɗi gwamnoni dake sanar da ranakun buɗe makarantu a jihohin su cewa su bi a hankali tukunna, kada maimakon ƙiba a samo rama.

Mustapha ya ce har yanzu wannan annoba na nan kuma tana addabar mutanen duniya. ” ganin cewa ana samun ƙarancin waɗanda suka kamu yanzu bai zama dalili ba na kuma banzatar da kokarin da aka yi a baya a saka rayukan yara cikin haɗari.

” Ko ƙasashe kamar su Jamus da suka buɗe makarantun su a wasu yankunan, duk sun faɗa cin tashin hankali domin annobar ta dawo musu suna ta koma suna rufe su kuma.

Mustapha ya ce ba Jamus ba kawai har da wasu ƙasashen Nahiyar Turai, suma sun sake dawo da dokar hana walwala saboda a a daƙile yaɗuwar cutar a dalilin bude makarantu da aka yi.

” Idan za a yi haƙuri a dan daga kafa zuwa gwamnatin Tarayya ta bayyana buɗe makarantun bayan ta shirya tsaf da yafi maimakon ace wasu gwamnoni na gaggawar buɗe makarantu a jihohin su.

Jihohin Oyo, Osun da Legas duk sun sanar da ranakun buɗe makarantu domin yara su koma karatu.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 143 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 19, Filato-35, Kaduna-21, FCT-13, Ebonyi-9, Adamawa-7, Enugu-7, Katsina-7, Edo-6, Kwara-5, Osun-3, Anambra-2, Kano-2, Niger-2, Ogun-2, Benue-1, Borno-1 da Sokoto-1

Yanzu mutum 54,008 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 41,638 sun warke, 1,013 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,357 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,138 , FCT –5,169, Oyo – 3,118, Edo –2,584, Delta –1,744, Rivers 2,141, Kano –1,727, Ogun – 1,648, Kaduna –2,141, Katsina –796, Ondo –1,539, Borno –741, Gombe – 723, Bauchi – 667, Ebonyi – 993, Filato -2,533, Enugu –1,162, Abia – 771, Imo – 527, Jigawa – 322, Kwara – 966, Bayelsa – 391, Nasarawa – 434, Osun – 782, Sokoto – 159, Niger – 243, Akwa Ibom – 278, Benue – 453, Adamawa – 228, Anambra – 216, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 262, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.

Share.

game da Author