Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 143 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 19, Filato-35, Kaduna-21, FCT-13, Ebonyi-9, Adamawa-7, Enugu-7, Katsina-7, Edo-6, Kwara-5, Osun-3, Anambra-2, Kano-2, Niger-2, Ogun-2, Benue-1, Borno-1 da Sokoto-1
Yanzu mutum 54,008 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 41,638 sun warke, 1,013 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,357 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,138 , FCT –5,169, Oyo – 3,118, Edo –2,584, Delta –1,744, Rivers 2,141, Kano –1,727, Ogun – 1,648, Kaduna –2,141, Katsina –796, Ondo –1,539, Borno –741, Gombe – 723, Bauchi – 667, Ebonyi – 993, Filato -2,533, Enugu –1,162, Abia – 771, Imo – 527, Jigawa – 322, Kwara – 966, Bayelsa – 391, Nasarawa – 434, Osun – 782, Sokoto – 159, Niger – 243, Akwa Ibom – 278, Benue – 453, Adamawa – 228, Anambra – 216, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 262, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.
An samu ƙarancin yawan waɗanda suka kamu da Korona a makon jiya cikin watanni uku
Ga dukkan alamu dai annobar Korona ta gangaro zuwa karshe domin bisa ga alƙaluman da ake samu a waɗannan kwanaki akwai yiwuwar Najeriya ta ci ƙarfin wannan cuta.
Sakamakon binciken da hukumar dakile yaƴuwar cututtuka ta kasa NCDC ta gabatar na mako-mako ya nuna cewa an fara samun ragowa a adadin yawan mutanen dake kamuwa da cutar.
A makon da ya gabata sakamakon ya nuna cewa mutum kasa 300 ne suka kamu da cutar a duk rana a kasar nan.
Gaba daya a wannan mako an samu karin mutum 1, 822 da suka kamu.
Zuwa yanzu mutum 53,865 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 41,513 sun warke, 1,013 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,339 ke dauke da cutar a Najeriya.
An yi wa mutum 402,070 gwajin cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a mutum 160 ne suka Kamu da cutar sannan jiya Lahadi ka Samu wasu mutum 138 suka kamu.
A cikin wannan mako jihar Filato ce jihar da ta fi samu yawan mutanen da duka kamu.
Har yanzu jihar Legas ita ce kan gaba a jerin jihohin kasar nan da suka fi yawan wadanda suka da mutum 18,188 sun kuma 202 sun mutu.
Daga Legas sai babban birnin tarayya Abuja, mutum 50 sun mutu sannan 5,156 suka kamu.
Najeriya ita ce kasa ta uku a jerin kasashen Afrika da suka fi fama da yaduwar cutar Mutum sama da miliyan 1.2 ne suka kamu da cutar a Nahiyar Afrika