Masanin abincin dake inganta garkuwan jiki Mohammed Sani-Hassan ya bayyana cewa Kashi 80 bisa 100 na cututtukan da ‘yan Najeriya’ suka fi fama da su na da alaka da rashin cin abincin da ya kamata.
Sani-Hassan ya ce rashin cin abincin dake inganta kiwon lafiya na daga cikin matsalolin dake haddasa cutar hawan jini, bugawar zuciya, shanyewar bangaren jiki, daji da sauran su.
Ya ce rage cin abincin dake kara kiba a jiki yawaita cin ganyayyakin da ake ci da ‘ya’yan itatuwa hanyoyi ne na kauce wa wadannan matsaloli.
Ma’aikatar kiwon Lafiya ta yi kira ga mutanen kasar nan da su rika motsa jiki a koda da yaushe, cewa rashin hakan na sa a kamu da cututtuka.
Ma’aikatar ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi da ya nuna cewa sama da matasa biliyan 1.4 a fadin duniya na gab da fadawa hadarin kumuwa da cututtuka masu tsanani a dalilin rashin motsa jiki da basu yi.
Binciken ya nuna cewa mutane da dama na kamuwa da cututtuka kamar ciwon Siga, Sankara, shanyewan bangaren jiki duk a dalilin rashin motsa jiki akai-akai.
Jami’ar WHO Regina Guthold ta ce kamata ya yi mutum ya sami minti 75 zuwa 150 a kullum rana yana motsa jikin sa.
Discussion about this post