‘Yan iskan gari ne suka yi wa jirgin Abuja zuwa Kaduna ruwan duwatsu ba mahara ba – Inji Hukumar NRC

0

Hukumar Jiragen Kasa ta Kasa ta bayyana cewa ba ba mahara bane suka kai wa jirgin kasa dake jigilar matafiya daga Abuja zuwa Kaduna. NRC ta ce wasu ‘yan iskan gari ne kawai suka rika harbin jirgin da duwatsu a lokacin da yake wucewa.

Wannan hari da matasan suka kai wa wannan jirgi yayi sanadiyyar fasa tagogin jirgin har guda biyu sannan kuma wata mata da take cikin jirgin ta sami rauni a jikin ta a dalilin wannan harin, kamar yadda wasu kafafen labarai suka ruwaito.

” Babu wani dan bindiga a cikin jirgin, idan ba haka ba ai da an ga harsasai a cikin jirgin.

” Wasu matasa ne suka fito suka rika jifar jirgin bayan an damke daya daga cikin su a lokacin da suka yi irin haka da rana. Sai suka fito da yawa suka rika jifan jirgin don a saki wanda aka kama.

Babban Darektan Hukumar, Fidet Okhiria ya kara da cewa tuni har sun sanar da jami’an tsaro domin su samar da tsaro a wannan hanya.

Haka kuma shima manajan hukumar na Kaduna ya bayyana inda matasan suka jejjefi jirgin. Ya ce a tsakanin Asham da kubwa ne matasan suka aikata wannan mummunar abu.

Ya karyata rade-radin da ake ta yi cewa wai mahara ne sufa far wa jirgin.

Share.

game da Author