Hukumar Zabe ta Kasa za ta gurfanar da wadansu malamai biyu na jami’a, da aka samu da laifin tafka magudin zabe.
INEC ta shaida wa manema labarai a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom cewa malaman wadanda dukkan su sun yi aiki a matsayin manyan jami’an zaben 2019 ne, sun baddala sakamakon zabe da gangan domin samar da sakamakon rinjayen kuri’u ga wanda ba shi jama’a su ka zaba ba.
Shugaban Sashen Yada Labarai da Wayar da Kai na INEC da ke Jihar Akwa Ibom, Odaro Aisien ne ya shaida wa manema labarai haka. Amma dai bai bayyana sunayen su ga manema labarai ba.
Ya ce malaman sun bayyana a gaban Kwamitin Bincike na INEC a Hedikwatar Hukumar Zaben.
INEC ta gabatar masu da hujjojin da suka hada da takardu, masu nuna cewa da gangar suka tafka laifin.
“Yayin da Hukumar Zabe ke jaddada cewa wannan laifi da malaman su ka aikata, ba ya na nufin dukkan sauran malamai haka su ke ba.
“Akwai wadanda da dama sun nuna jajircewa, kwarewa da kuma kishi wajen gudanar da ayyukan su na zabe. Amma hukunta wadannan bara-gurbin zai kara zama darasi.”
Sannan kuma INEC ta bayyana korar ma’aikatan ta su uku da aka samu da laifin murdiyar zabe.
Kwamishin Zabe na Kasa a Jihar Akwa Ibom, Mike Igini, wanda ya yi suna wajen kin yarda a yi danniya ko murdiyar zabe, ya sha karo da masu son ko ta hakin kaka su yi danniya a lokutan zabe a jihar.