Ƙasar Birtaniya ta ce ba za ta amince da tafka maguɗi a zaɓukan gwamonin jihoin Edo da Ondo, wanda za a yi a cikin watan Satumba da Oktoba mai zuwa ba.
Ta ce ba za ta lamunci duk wata kisisina da munakisar da za a yi sanadiyyar gurgunta dimokraɗiyya a Najeriya ba.
Daga nan ta yi alkawarin soke bizar shiga ƙasar da kuma kwace tarin dukiyar duk wanda ya yi sanadiyyar hargitsa zabe ta yin amfani da hanyoyin magudi ko tayar da rikici a lokacin zabe.
Jakadar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja.
“Mu na biye sau-da-kafa kan dukkan abin da ke faruwa dangane da shirye-shiryen zabukan Jihar Edo da Ondo, wadanda INEC za ta yi a ranar 19 Ga Satumba da kuma 10 Ga Oktoba.
“Wannan zabe zai zama ma’aunin zaman dimokradiyya sahihiya da gindin ta a Najeriya, ko kuma akasin haka.
“Za mu tura masu sa-ido a jihohin biyu domin su ga yadda zabukan za su gudana. Mun yi taro da shugabannin PDP da na APC, inda mu ka jaddada cewa duk wanda aka kama da laifin gurgunta sahihin zabe, to za mu hana shi bizar shiga Ingila da kuma kwace ilahirin dukiyar sa da ke Birtaniya.”
Wannan jawabi na ta ya zo ne kwana daya bayan Amurka ta tofa wa wasu manyan ‘yan siyasar kasar nan kasa a ido, inda ta haramta musu shiga kasar ta.
Amurka ta bayyana haramta wa wasu manyan Najeriya masu yawa shiga kasar, bayan samun su day hannu wajen yin magudin zabe a Jihar Kogi da Bayelsa, a zaben 2019.
Yayin da saura kwanaki uku a yi zaben gwamnan Edo, manyan ‘yan siyasa daga PDP da APC na ci gabada da yin tururuwa zuwa Benin, babban birnin jihar Edo.