Gwamnatin Kano ta gyara makarantun kwana na Almajirai uku da naira miliyan 159 a jihar

0

Gwamnati jihar Kano ta bayyana cewa ta kashe naira miliyan 159 wajen gyaran wasu makarantun kwana na almajirai a jihar.

Kwamishinan ilimin jihar Sanusi Kiru ya sanar da haka a wata takarda da jami’in hulda da jama’a ta ma’aikatar Aliyu Yusuf ya rabawa manema labarai ranar Laraba.

Kiru ya ce makarantun da aka gyara na kananan hukumomin Madobi, Bunkure da Bagwai.

Ya ce za a samar da katifu, gina rijiyar burtsatse, da masallaci a wadannan makarantu.

“Yin haka na cikin aiyukkan inganta makarantun almajirai da gwamnati ke kokarina yi a jihar.

Idan ba a manta ba a watan Mayu ne Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa duka gwamnonin Arewa sun amince lallai lokaci yayi da za a kau da tsarin karatu irin na Almajirci a yankin kwata-kwata, kuma kowa na aiki tukuru don ganin haka ya tabbata.

” Mun dade muna neman yadda za a kauda da wannan tsarinn karatu na Almajirci. Almajirci bai kari su yaran da komai ba, bai kari yankin da komai ba sannan bai kari Najeriya da komai ba.

” Gara a ace an dauki yara 200 a makarantun Boko ana koyarda su yadda za su amfani kansu da al’umma, maimakon a kyale su suna watangaririya a manyan tituna suna barec-baracen abincin da zasu ci. Kowani irin salon karantarwa ne ya fi wannan tsari na Almajirci kuma za mu tabbata ya zo karshe yanzu.

Share.

game da Author