HUKUNCIN KISA: Mawaki Aminu Shariff ya daukaka kara

0

Mawakin nan da aka yanke wa hukuncin kisa ya kalubalanci wannan hukunci a kotun daukaka kara, yana mai kira ga kotun ta soke hukuncin da kotun shari’a ta Kano ta yanke masa.

Idan ban a manta ba kotun sharia a Kano ta yanke wa mawaki Shariff hukunci kisa ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin yi annabin Mohammadu SAW izgilanci a wakar sa.

Sharif ya ce yana kalubalantar wannan hukunci ta kotun sharia’a ne ganin cewa Najeriya na da dokokin da ta ke bi kuma take amfani da na Kwanstitushon kuma ba da wannan kundin na Kwanstitushon aka bi aka yanke masa hukunci ba.

” Ban amince da wannan hukuncin kotun shari’a ba saboda Najeriya ba da dokar musulunci ta ke aiki ba. Idan da dai kasar da ake amfani da hukuncin musulunci tsagwaran ne shine za yanke irin wannan hukunci kuma ta zauna amma Najeriya na da Kwansitushon, yanke wannan hukunci ya saba wa wannan kundin.

Shariff ya ce an saba wa dokar Najeriya don anyi amfani da wani abu dabam wajen yanke masa hukunci maimakon dokar kasa wanda da ita ake aiki da, wato ‘Kwansititushon.’

Tun bayan wannan waka da Shariff yayi zaman lafiya ya kare masa, domin har gidan mahaifin sa an nemi a banka wa wuta a Kano amma gidan ya sha da kyar daga hannun matasa.

Bayan haka kuma daga baya mahaifin sa yayi hannun riga da shi tun bayan sakin wannan waka.

Gwamna Ganduje ma ba a barshi a baya ba wajen nuna fushin sa ga wannan matashi. Ya shaida cewa da zaran bai yi nasa a Kotu ba lallai zai rattaba hanna a takardar hukuncin kisa da kotun musulunci ta yi masa a Kano.

Share.

game da Author