Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Hadi Sirika ya bayyana cewa gwamnati ta hana wasu jirage sauka a tashoshin jiragen saman kasar.
Wadannan jirage sun hada da da jirgin KLM, Air France, Etihad, Rwandair, Lufthansa, TAAG Angola Airlines, Air Namibia,da Royal Air Maroc.
Sirika yace dama ya lashi takobin sai an dakatar da wasu jirage sauka a tashoshin jiragen Najeriya saboda suma irin dokar da saka wa na Najeriya kenan.
Ya bayyana wadanda gwamnati ta amince da su kamar haka, Middle-East, British Airways, Delta Airlines, Qatar Airways, Ethiopian Airlines, Egyptair, Air Peace, Virgin Atlantic, Asky, Africa World Airways (AWA), Air Cote-d’Ivoire, Kenya Airways, Emirate, da Turkish airlines.
A karshe ya shaida cewa an bi doka kafin aka sanar da wadanda za su rika sauka da tashi a kasar.