Babban darektan hulda da jama’a na Hukumar Kula da jami’oi na Kasa, NUC Ibrahim Yakasai ya bayyana cewa hukumar ta gamsu da ayyukan da jami’ar Maryam Abacha ke yi a jami’ar da ke Hotoro da Gwarzo, a jihar Kano.
Yakasai ya jagoranci tawagar hukumar NUC domin yin ziyarar aiki da gani wa ido a zangon karshe kafin a mika wa jami’ar lasisin fara aiki.
” Mun gamsu da abinda matuka gani matuka kuma tabbas mahukuntan jami’ar na aiki tukuru wajen ganin an kammala kakkafa duk abinda ake bukata domin fara aiki a jami’ar.
Bayan wannan ziyara, PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da shugaban jami’ar Maryam Abacha, Farfesa Adamu Gwarzo, inda ya shaida mata cewa yanzu dai suna jiran hukumar jami’oi ne tu basu takardar amincewa ta fara aiki.
” Jami’ar Maryam Abacha ta Najeriya dake Kano, za ta taka rawar gani matuka idan ta fara aiki domin kuwa daliban mu za su fita da bam da na wasu jami’o’in. Shirin da muke yi ba na wasa bane. Baya ga karatun darussa za mu tabbata daliban mu za su iya yaren faransanci baya ga turanci da za a rika koyar dasu da shi.
Jami’ar Maryam Abacha ce jami’a ta farko a Jamhuriyar Nijar da take karantar da dalibanta da harshen turanci. Sannan kuma dalibanta sun shahara matuka a duniya.
A jihar Kaduna ma jami’ar ta bude kwalejin koyan aikin likitanci da na ungo zoma da tuni har ta fara aiki gadangadan.