HUKUNCIN KISA: Matawalle ya nada Alaramman da ya tsallake rijiya da baya a Saudi Hadimin sa

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya nada Alaramma Hafeez Ibrahim da ya tsallake rijiya da baya bayan an kama shi bisa zargin mallakin wani jaka dankare da muggan ƙwayoyi a kasar Saudi.

Kakakin gwamna Matawalle, Zailani Bappa ya bayyana cewa saida Ibrahim ya sheka ra hudu tsare a kasar Saudiyya mahukunta na tuhumar sa kan zargin kama shi da muggan ƙwayoyi da aka yi cikin kuskure.

An kai Ibrahim Kotu har sau biyu kuma duk suna yanke masa hukuncin kisa.

Kotun farko ta yanke masa hukuncin kisa, kotu ta biyu ta jaddada hukuncin da kotun farko ta yanke.

Haka dai yayi ta fama har zuwan gwamna Matawalle. Daga nan ne fa ya aika da tawaga na musamman zuwa kasar domin a samu a wanke alaramma Ibrahim daga zargin yin dakon muggan ƙwayoyi zuwa kasar Saudiyya.

Bayan haka Matawalle yayi hayan ƙwararrun lauyoyi tun a lokacin domin kare Ibrahim a kotu da wanke shi daga zargin da mahukuntan kasar ke masa sannan su tabbatar wa kotu cewa wannan jaka da aka kama ba na Hafeez Ibrahim bane.

Kotun Saudi ta sallami Ibrahim bayan tabbatar da lallai ba shi bane ke da mallakin wannan jaka da ake zargin sa da shce. An sake shi tun a farkon wannan shekara ne amma bai samu daman dawowa Najeriya ba saboda dokar Korona na hana tashi da sauka a kasar da kasashen duniya.

Ibrahim ya sauka Najeriya ranar Talata daga nan sai ya zarce garin Zamfara in da gwamna Matawalle ya mika shi ga Iyalansa da suka kosa su ganci bayan shafe shekaru kusan hudu ba su tare.

A karshe gwamna Matawalle ya nada Ibrahim hadiminsa na musamman.

Share.

game da Author