Yadda Soja ya bindige abokin aikin sa a Bama

0

Hedikwatar tsaron rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa wani soja dake aiki bataliya ta biyu ya bindige abokin aikinsa a Bama jihar Barno.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Sojojin Najeriya, Sagir Musa, ya sanar da haka a wani takarda da ya raba wa manema labarai a karshen makon jiya.

Wannan mummunar abu ya auku ne ranar Laraba a garin Bama Jihar Barno.

Musa ya ce sojan ya bindige abokin aikin sa dake tsaye a gaban ofisohin hedikwatar bataliyar a lokacin yana amsa wayar sa bayan an kira shi.

Musa ya cetuni har an damke wannan Soja da yayi kira sannan an ajiye gawar wanda aka kashe a asibitin dakin ajiye gawa dake asibitin Sojoji a bama.

Ya ce rundunar ta yi kira iyayen mamacin domin yi musu ta’aziya sannan ta ci gaba da gudanar da bincike domin domin sanin dalilin da ya sa wannan soja ya aikata haka.

Wannan ba shine karon farko da Soja kan dana bindiga ya harbe kansa ba ko wani dake kusa da shi, wato abokin aikin sa. A kwanankin baya akwai wani Soja mai suna Adegor Okpako, dake aiki da Bataliya ta 192 a Gwoza, ya dirka wa wani abokin aikin sa bindiga sannan ya karkata bindigar shima ya dirka wa kansa, gaba dayan su suka sheka lahira.

Share.

game da Author