Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 386 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –65, FCT-130, Ondo-37, Osun-29,Filato-23, Rivers-15, Enugu-14, Nasarawa-12,Bayelsa-11, Ebonyi-11, Ekiti-9, Oyo-8, Edo-8, Abia-6, Ogun-3, Katsina-3, Imo-1
da Adamawa-1.
Yanzu mutum 43,537 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 20,087 sun warke, 883 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,567 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,186 FCT – 3,933, Oyo – 2,768, Edo – 2,300, Delta – 1,510, Rivers 1,806, Kano –1,597 , Ogun – 1,397, Kaduna – 1,457, Katsina –745, Ondo – 1,192 , Borno –613, Gombe – 607, Bauchi – 560, Ebonyi – 796, Filato – 1,411, Enugu – 821, Abia – 551, Imo – 469, Jigawa – 322, Kwara – 753, Bayelsa – 339, Nasarawa – 329, Osun – 553, Sokoto – 153, Niger – 224, Akwa Ibom – 221, Benue – 346, Adamawa – 164, Anambra – 135, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 141, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 45.
KIRA GA MATASA: Cutar Korona har kisa ta na yi idan ta Kama matashi – Shugaban WHO
Shugaban Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus ya gargadi matasa da ke cewa kwayoyin cutar Korona ba zai iya kama su ba da su daina wannan zato, yana mai cewa ba kama matashi ba ma kawai har kisan sa zai iya yi idan bai kiyaye ba.
Bayan haka kuma ya shaida cewa lokaci yayi da kasashen duniya za su koyi shirin zama dindindin da kwayoyin cutar Korona.
Dole ne mu koyi rayuwa da wannan cuta tare da ɗaukar matakai domin mu rayu, tare da kare kanmu da sauran jama’a.
Sannan kuma ya yabawa kasar Saudiyya kan irin matakan da ta ɗauka yayin gudanar da Aikin Hajjin bana.