TATTAUNAWA: Yadda Najeriya za ta bunkasa noman tsallake-siradin-yunwa a yanayin kuncin tattalin arziki

0

A cikin wannan muhimmiyar tattaunawa da PREMIUM TIMES ta yi daya daga cikin jiga-jigan kamfanin Tuntubar Bunkasa Dabarun Noma Abinci Mai Gina Jiki, Sahel Consulting Agriculture and Nutrition Ltd, Ndidi Nwuneli, ya bayyana yadda Najeriya za ta iya amfani da dabarun da za ta bunkasa noma domin tsake siradin yunwar da ta tunkaro kasashen duniya gadan-gadan, sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus.

PT: Shin ta ya ka ke ganin za a iya cin nasarar wadatar abinci da kuma fatattakar yunwa a Najeriya?

NWUNELI: To matukar dai ba mu yi gaggawa ba, duk wani kokarin hada hannun da za mu yi domin nasarar ganin an fatattaki yunwa nan da shekarar 2030, zai zama almara kawai.

Sama da mutum milyan 821 sun fuskanci fushin yunwa a 2019. Kuma akasari rikice-rikice ne da kuma tashin-tashinar da ke wanzuwa a cikin al’umma suka haddasa wannan matsalar yunwa.

Shirin Bunkasa Abinci a Duniya (World Food Programme, WFP), ya kiyasta cewa akalla mayunwata yanzu a duniya sun ma haura mutum bilyan daya. Abubuwan da suka kara haddasa haka kuwa sun hada da cutar Coronavirus, canjin yanayi da ya tsananta, karyewar arzikin da ta shafi kusan komai ns duniya bagatatan, ciki har da rubdugun rasa aikin yi’ da ya buwayi duniya a yanzu, raguwa da karancin shigar kudade a hannun jama’a da kuma karyewar da gadar hada-hadar kasuwanci da saye da sayarwa ta shafa.

To duk wadannan matsaloli sun shafi Najeriya, bugu da kari ma har da gagarimar matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Sannan kuma tsarin samar da abinci a kasar nan, ba a bisa sahihiyar turba ya ke ba. Har yau ba mu cin moriyar fasahar zamani a fannin noman kasar nan. Ga yunwa da fatara. Shi ya sa idan irin matsala ta yunwa ko karancin abinci ta fantsama a nan, sai ka ga kawai ta zama kamar iska ya iske kaba na rawa, sai kawai ya yi gaba da ita.

Don haka samun nasarar bunkasa kasa da abinci abu da ke bukatar hadin guiwar gwamnati, ‘yan kasuwa, manoma daidaikun jama’a da duk sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma.

PT: Ko akwai wani darasi da Najeriya za ta iya koya a lokacin cutar Coronavirus da kuma bayan an dakile ta gaba daya?

NWUNELI: Ai ka ga cutar Coronavirus ta haddasa karancin abinci, saboda komai ya tsaya cak a duniya. Manoma sun kasa samun zuwa wurin aikin noman su. Wadanda ke da amfanin gona kuma ba su samun damar su kai kasuwa su sayo. Kuma ba su samun sukunin sayen kayan amfanin noma a kasuwanni.

Kayan da ake shigowa da su na fannin noma daga kasashen waje, suka yanke saboda an sufurin jiragen sama da na ruwa kasashe.

To wannan matsala kuma sai ta haddasa masu wasu kayan abinci ko nau’ukan masarufin abinci rika boyewa. Hakan sai ya kawo tsadar abinci ko kayan abinci, inda a wasu kasashen ma irin Najeriya, Karin farashin da aka rika samu sai da ya rika nunkawa.

To akwai bukatar a tantance komai a kasar nan, musamman yawan kanana da manyan manoma da sauran su da kuma abin da suke nomawa. Sannan akwai ma bukatar a yi kididdigar yawan ‘yan Najeriya sukutum.

Kai, ya kamata ma mu san yawan manoman birni da na karkara, a san yawan cima-zaune, a lissafa yawan yara ‘yan kasa da shekaru biyar da kuma ‘yan sama da shekaru 60. A San yawan ‘yan kasuwa, ‘yan tireda, yawan gidajen sayar da abinci da yawan bankuna.

Mafita daga karancin abinci a Arewacin Najeriya – Nwuneli

PT: Rahoton Matsalar Karancin Abinci a Duniya (Global Report on Food Crisis) ya tabbatar da cewa mutum sama da milyan 75 na fama da tantagaryar yunwa a duniya. Daga cikin su mutum sama da milyan 5 a Arewacin Najeriya. Shin ina mafita daga wannan?

NWUNELI: Akwai rahoton gungun masana harkar noman yadda za ta kori yunwa nan da 2030, wato Catalyst2030, wanda ni ina cikin su. Mun rubuta wa shugabannin Afrika cikakken daftarin da za su yi aiki da shi da za a samu mafita.

Mu dawo batun Arewa. Ya kamata a Arewa a kafa Kwamitin Shawo Kan Matsalar Yunwa da gaggawa, wanda zai kunshi duk masu ruwa da tsaki a harkokin noma da sauran harkokin da ke da kusanci ko jibintar rayuwar manoma.

Kwamitin ya kunshi kungiyoyin manoma, babban jami’in gwamnatin tarayya, bangaren kiwon lafiya, wakilan harkar noma, kimiyya da fasaha, masu zuba jari, bangaren ilmi, yadda za a samu kudaden ayyukan noma, kungiyoyin addinai, cibiyoyin harkokin noma.

Sannan a tabbatar da samun ingantaccen tsaro da tallafa wa manoma. Kuma a rungumi dabarun noma na fasahar zamani.

PT: Rahoto ya nuna kashi 97 bisa 100 na harkokin hada-hadar sun samu cikas sanadiyyar cutar Coronavirus. Shin ya ka ke ganin harkokin kasuwanci da tattalin arziki zai sake murmurewa?

NWUNELI: A yi haramar rungumar dabarun noma ta hanyar fasahar zamani. A kara kirkiro hanyoyin bunkasa harkokin noma da kasuwanci. A karfafa dangantakar cinikayya tsakanin harkokin noma da kuma masana’antu.

Share.

game da Author