Farashin kayan abinci ya kara hauhawa da matsanancin tsada, cikin watan Yuli a Jihohin Zamfara, Kogi da Yobe.
Jadawakin kididdigar alkaluman farashin kayan abinci da na masarufi da Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta fitar ne ya nuna haka.
Rahoton ya ce, tsakanin watan Yuni zuwa Yuli, kayan abinci sun yi tsadar da ba su taba yin kamar ta ba a baya, a Jihar Zamfara.
Farashin a cewar NBS ya karu da kashi 3.40. a Jihar Kogi Kuma ya karu da kashi 3.32. Sai kuma Jihar Yobe, inda farashin ya karu da kashi 3.00.
A jihohin Neja da Ogun kuwa har ma da Lagos, farashin bai karu da yawa ba kashi 0.44, sai kuma da kashi 0.41 a Lagos.
Rahoton ya ce tsakanin watan Yuli 2019 da watan Yuli na 2020, farashin kayan abinci ya ksru da kashi 20.09 a Kogi, kashi 19.28 a Sokoto, sai kuma kashi 18.05 a Jihar Filato a cikin Yuli.
Mutum milyan 54 ba su da aiki a Najeriya
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga bayanan NBS, wato Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), inda ta fitar da lissafin cewa akwai kashi 27.1 na yawan ‘yan Najeriya da ba su da aikin yin da za su rika samun kudin abincin yau ko na gobe.
Wannan kididdiga na nufin idan yawan jama’a a Najeriya sun kai milyan 200, to milyan 54,200 ba su da aikin yi kenan.
NBS ta ce wannan Kididdiga ta yawan adadin wadanda aka tababtar ne a watannin Aprilu, Mayu da Yuni na cikin 2020.
Rabon da NBS ta yi wannan kididdiga tun wadda ta yi cikin watannin Yuli, Agusta da Satumba na 2018, inda a lokacin aka samu kashi 23.1 na ‘yan Najeriya duk ba su da aikin yi.
Kafin wannan kuwa a lissafin watannin Oktoba, Nuwamba da Disamba, 2018, kashi 18.8 ba su da aikin yi.
Ya zuwa watanni ukun tsakiyar 2018 ne adadinya karu zuwa kashi 23.1, sai kuma yanzu cikin 2020 da adadin ya karu zuwa kashi har 27.1.
Annobar cutar Coronavirus ta zuzuta matsalar tabarbarewar tattalin arziki, inda manyan masana’antu suka rika sallamar ma’aikatan su, wasu kuma su ana zaftare musu albashi.
NBS ta ce yawan majiya karfin iya aikin neman kudi a Najeriya sun karu daga mutum milyan 111.1 cikin 2017 zuwa milyan 115.5 cikin tsakiyar 2018.
Sai dai kuma NBS ba ta fadi adadin yawan cima-zaunen da ke Najeriya ba, ballantana a san yawan su.
Discussion about this post