Yadda hada-hadar amfanin gona ta tallafa wa rayuwar manoman Najeriya

0

Bala Idris ya cika da farin ciki, ganin yadda amfanin gonar sa ya bunkasa kuma ya samu kudi sosai da harkar noman shinkafa a cikin 2018.

Kafin wannan shekarar kuwa, hekta daya da Bala ke da ita, ba ma iya noma ta ya ke yi ba. Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho da wakilin mu ya yi tattaunawa da shi.

Kafin ya samu wannan nasibin noman shinkafa kuwa, a kullum ya na zaman zullumin yadda zai iya ciyar da iyakin sa, saboda rayuwar hannu-baka-hannu-kwarya da suke yi.

Neman mafita daga kangin talauci ya sa Bala gaganiyar hanyar da zai tsira da mutuncin sa, ta hanyar samun hanyar da zai bunkasa noma kayan amfanin gona na sayarwa a cikin 2018, ta hanyar taimako da AFEX cikin 2018.

Tun a kakar farkon da ya shiga tsarin AFEX ya fara ganin faraga a harkar noman sa. Ga yawan amfanin gona kuma ga nagarta sosai.

A Kano Bala ke da gona mai fadin hekta daya, amma da kyar ya ke iya noma buhun shinkafa 20 mai nauyin kilogiram 100.

Amma yayin da Bala ya shiga tsarin AFEX, sai ga shi ya na noma har buhu 40 a wannan hekta daya, kuma babban buhu mai nauyin kilogiram 100 din dai.

“Rajista na yi a matsayin manomi da tsarin AFEX a Kano, sai aka ba mu kayan noma a matsayin lamuni, aka ce za mu biya idan mun girbe amfanin gonar mu.” Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Hada-hadar cinikin kayan gona a Najeriya

AFEX Commodities Exchange Limited (AFEX) ne ke gudanar da Harkokin Cinikayyar Amfanin Gona, tare da hadin guiwar Ma’aikatar Harkokin Noma da Bunkasa Karkara ta Kasa, bisa tafiya a karkashin masu zuba jari na kamfanonin Berggruen Holdings, Heirs Holdings, Ngali Holdings da kuma 50 Ventures.

Cikin 2014 aka kirkiri wannan tsari, wanda manoma ke kai ajiyar amfanin gona ana adana musu a manyan rumbuna, sannan a ba su lamunin kudade.

Sai amfanin gonar ya fara tsada ne za su sayar, su biya lamuni.

AFEX wani bangare ne na Africa Exchange Holdings da aka kafa a 2012, domin bunkasa hada-hadar kasuwancin kayan gona a Afrika ta Gabas da Afrika ta Yamma.

Hususan ya fi ta’allaka ne wajen hada-hadar adana amfanin gona domin hana shi lalacewa da wuri.

A tattaunawar da manajan AFEX, Innocent Ihopo ya yi da PREMIUM TIMES, ya ce su na amincewa da manoma ne a kungiyance. Amma da zarar an amince da manoman, to kowa da shi kadai karan kan sa za a rika hulda da shi.

Ya ce akwai jami’ai da ke yi wa manoman rajista a kungiyance kafin a fara hulda da kowa shi kadai.

Ya ce suna da rumbun ajiyar bayanai na yanar gizo da suke tantance bayanan da duk su ke bukatar samu daga kowane manomi.

Bayanan sun hada da lambar sirri ta ajiyar banki, wato BVN da suna da adireshi da ranar haihuwa da duk sauran bayanan da suka wajaba a nema a hannun manomi.

Sannan kuma ana bukatar manomi ya bayar da kashi 15 na adadin kudin kayan noman da za a ba shi ramce tukunna.

“Dukkan wadannan bayanai da kashi 15% na kudin, manomi zai fara bayar da su ne kafin a ba shi lamunin.” Inji shi.

Akwai yarjejeniyar abin da manomi zai biya idan ya nome amfanin gonar sa. Sannan kuma akan gurfanar da wanda ya ki biyan na sa bashin noman.

Ko kuma a kai rahoton manomi Ofishin ‘Yan Sanda ko Ofishin ‘Yan Bijilante.

Share.

game da Author