Wani gagarimin hari ta jiragen yaki da sojojin Operation Lafiya Dole suka Kai Kan Boko Haram, an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da banka wa mabuyar su da wurin ajiye makaman su wuta a Tumbuma Babba da Boboshe a cikin Jihar Barno.
Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ce ta fitar da wannan sanarwar karkashe ‘yan Boko Haram din a Tafkin Chadi da kuma cikin Dajin Sambisa.
Babban Jami’in Yada Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar JohnEnenche ne fitar da wannan sanarwar a Abuja, ranar Litinin.
Ya ce an kai farmakin farko ne a ranar 16 Ga Agusta, bayan an tabbatar da hango sansanonin da ‘yan Boko Haram din a Tafkin Chadi da kuma Dajin Sambisa.
Ya ce farmakin da aka kai kan Boko Haram a Tumbuma Baba, wani tsibiri ne da ke cikin Tafkin Chadi, wanda Boko Haram suka yi kaka-gida a kan sa.
‘Yan leken asiri suka tabbatar da cewa ‘yan ta’adi ISWAP sun yi sansani a cikin surkukin bishiyoyin da ke kan tsibirin.
“Nan da nan aka tura wasu zarata a cikin jirgin yaki, suka ragargaje sansanonin da lalata kayan fadan su da kuma yin nasarar kashe da dama a cikin su.
“An kuma karkashe wasu ‘yan ta’adda masu yawa a farmakin da aka kai musu a Boboshe, wani kauye da ke Gabacin Sambisa, inda jiragen yaki suka yi musu luguden wuta.”