SERAP ta nemi kotu ta tilasta Buhari bayyana abin da ya yi da naira bilyan 800 da aka kwato daga hannun barayin gwamnati

0

Kungiyar Kwato Hakki da Sa-ido Kan Hana Rashawa (SERAP), ta maka Shugaba Muhammadu Buhari a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, inda ta nemi ta tilasta wa Shugaba Muhammadu Buhari bayyana sunayen wadanda gwamnatin sa ta kwato zunzurutun naira bilyan 800 daga hannun su.

Buhari da bakin sa ya bayyana cewa gwamnatin sa ta “kwato naira bilyan 800 daga hannun barayin gwamnati.

Buhari ya yi wannan jawabi a cikin takardar da ya karanta, a ranar 12 Ga Yuni, ranar Dimokradiyya, inda ya kara da cewa, “Ana ci gaba da zuba kudaden cikin ayyukan raya kasa da gwamnati ke aikatawa.”

Cikin karar da SERAP ta shigar, mai lamba: FHC/ABJ/CS/1064/2020, ta nemi kotu ta tilasta Buhari ya bayyana wasu abubuwa kamar haka.

1. Shugaba Buhari ya bayyana sunayen barayin gwamnati da aka kwato naira bilyan 800 a hannun su.

2. Shugaba Buhari ya bayyana naira nawa aka kwato gs kowane mutum daya.

3. Shugaba Buhari ya bayyana ranakun da aka karbo ko nawa ne daga hannun kowane barawon gwamnati.

4. Buhari ya fito ya bayyana dukkan ayyukan da ya ce an yi da kudaden da kuma inda aka yi ayyukan.

5 Sannan ya bayyana farahin da aka bayar da kowace kwangilar da aka biya a cikin kudaden.

6. Kuma Buhari ya bayyana garuruwa da wuraren da aka yi ayyukan, domin SERAP ta je ta gani da ido, sannan ta tabbatar.

7. SERAP ta kara nemsn kotu ta umarci Buhari ya gaggauta bayyana sunayen wasu daidaikun mutane da Gwamnatin Tarayya ta tura wa jimillar kudi har naira bilyan 51 a cikin 2019.

Lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare da Opeyemi Owolabi ne su ka shigar da karar a madadin SERAP.

Sauran wadanda aka hada tare da Buhari aka maka a kotu, sun hada da Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami da kuma Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed.

SERAP ta ce ‘yan Najeriya na da hakkin sanin yadda aka yi da kudaden da kuma wadanda suka tsiyata kasar nan, tare da sanin ko adadin naira nawa kowanen su ya sata.

Sannan kungiyar ta ce ‘yan Najeriya ba za su gamsu da sahihancin kalamin Buhari ba, da ya ce ana amfani da kudaden ana yin ayyukan raya kasa da su, har sai sun ga yadda aka kashe kudaden dalla-dalla.

Share.

game da Author