Kwamitin gudanarwar Jami’ar Legas ya dakatar da shugaban jami’ar

0

Kwamitin gudanarwar jami’ar Legas ya tsige shugaban jami’ar Oluwatoyin Ogundipe.

Mambobin kwamitin gudanarwar jami’ar sun yi zama ta musamman a hedikwatar hukumar Jami’oi ta kasa a Abuja ranar Laraba inda suka zartar da tsige shugaban jami’ar.

Kwamitin ya ce ana zargin Masta Ogundipe, shugaban jami’ar da yin sama da fadi da kudaden jami’ar.

Kakakin shugaban kwamitin gudanarwar, Wale Babalakin, Mikhail Mumuni, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da haka.

Idan ba a manta ba an soke bukin yaye dalibai na shekarar 2020, awoyi kadan kafin a fara bukin.

Babban dalilin dakatar wannan bukin kuwa shine wai don shugaban jami’ar bai bi da su dalla-dalla ba lokacin da ake shirya bukin.

Hakan yasa ministan Ilimi ya dakatar da Ogundipe a bisa dalilin korafin da suka mika masa.

Sai dai kuma shugaban jami’ar Ogundipe ya bayyana cewa yana na daram a matsayin shugaban Jami’ar.

Ya ce kamar yadda kowa ya karanta haka shima ya karanta wai an dakatar da shi.

Share.

game da Author