Kotun majistare dake Ikeja jihar Legas ta daure Wani Happiness Sunday mai shekaru 21 a kurkuku bayan ta kama shi da laifin yi wa wasu Yara biyu mace da namiji fyade.
Dan sandan da ya shigar da Kara, Christopher John ya ce Sunday mazaunin Magodo ne a Legas sannan an kama shi da laifin yin lalata da ‘ya’yan makwabtansa mace da namiji masu shekaru 8 da 10 a dakinsa.
John ya ce Sunday ya yi lalata da wadannan Yara tun a watan Mayu.
Yace Happiness Ya kan rudi yaran ne da dan alawar tsinke ko kuma karago, alkaki ko dakuwa sai ya sulale da su dakin sa daga nan ya ya fitsarar sa. Yan macen gobe namiji.
Alkalin kotun P.E. Nwaka ya Yi watsi da rokon sassauci da Sunday ya yi, ya yanke masa hukuncin zaman kurkuku.
Nwaka ya ce Sunday zai zauna kurkuku har Sai kotu ta kammala yin shawara da sashen gurfanar da masu aikata laifuka irin haka ta rundunar ‘yan sandan jihar.
Za a ci gaba da shari’a ranar 23 fa watan Satumba.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne ‘yan sandan jihar Ogun suka damke wani Fasto mai suna Ebenezer Ajigbotoluwa da ake zargin yi wa Ya da Kanwa ciki sannan da damfarar uwar su naira miliyan 2.
” Shi dai wannan fasto ya yi alkawarin warkar da wadannan ‘yan mata ne daga shaidanun aljanu da suka shafe su. Daga nan sai ya umarci mahaifiyar su ta dawo da iyalanta kaf harabar cocin domin aiki yayi kyau sannan ya ce ta bashi naira miliyan 2 domin aiki za a yi sosai.