Gwamnonin Najeriya sun roki Shugaba Muhammadu Buhari ya ba su tulin kudaden da za su yi amfani da su wajen shawo kan matsalar tsaro a jihohin su.
Gwamnonin sun mika wa Buhari wannan babban kokon barar a lokacin taron Majalisar Tsaron Kasa, wadda Buhari ya jagoranta a ranar Talata a fadar sa.
Gwamnonin sun yi taron ne tare da dukkan shugabannin bangarorin tsaron kasar nan.
Shi ma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya halarci taron.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Fadar Shugaba Buhari ya fitar, Garba Shehu ya ce Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na Ekiti, shi ne ya gabatar da rokon ga Buhari.
Fayemi ya ce gwamnonin Najeriya na bukatar kudaden da za su mulmula, su maida su gudumar dukan matsalar tsaro, tunda su ma sun amince wa Buhari ya kamfaci dala biliyan 1 daga Asusun Rarar Ribar Danyen Mai domin sayo makamai na zamani da za a yi yaki da matsalar tsaro da su a cikin kasar nan.
A cikin watan Afrilu gwamnonin Najeriya sun roki Babban Bankin Najeriya, CBN ya daga musu kafa ta hanyar dakatar da cirar musu kudade ana rage dimbin bashin da ake bin su.
Sun ce dakatar da cire musu kudaden zai dan kara wa aljifan jihohi nauyin saukake musu halin kuncin da annobar Korona ta janyo a kasar nan.
A na sa bayanin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya bayyana matsalar fatara da talauci, rashin aiki ko sana’ar dogaro da kuma karancin amana tsakanin sojoji da fararen hula da kuma antayo kananan makamai a cikin jama’a.”
“Gwamnan ya kuma bayyana matsalar rashin tsimakekeniyar tsare-tsaren ayyukan tsaro tsakanin sojoji da sauran bangarorin tsaro.
“Daga nan ya roki Shugaba Buhari ya duba yiwuwar bayar da kudaden ga jihohi domin ceto su, tare da yin la’akari da dimbin dukiyar da su ma suka kashe wajen mara wa sojoji da ‘yan sanda baya domin inganta tsaro.”
Matsalar tsaro sai kara tabarbarewa ta ke yi a dukkan jihohin kasar nan.
Yayin da Boko Haram ke kai hare-hare a garuruwan Barno da makwautan jihohi, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane na ci gaba da kai hare-hare a Arewa maso Yamma.
Yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, ya zama ruwan dare a yankuna da dama na kasar nan.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Gwamnatin Amurka ta gargadi ‘yan kasar ta, kwanan nan cewa kada su kuskura su ziyarci wasu garuruwa da jihohi da dama a Najeriya, wadanda ta ce akwai matsalar tsaro cikin su.
Discussion about this post